1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton Goldstone

Tijani LawalOctober 15, 2009

Ra'ayin Palasɗinawa da Larabawa akan rahoton Goldstone

https://p.dw.com/p/K6q2
Richard Goldstone na gabatar da rahotonsaHoto: AP

Palasɗinawa da Larabawa sun bayyana rashin amincewar su da shawarar da kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayar dake buƙatar Palasɗinawa da Israila su kafa kwamitocin cikin gida domin duba zargin aikata laifukan yaƙin da rahoton majalisar ta ɗinkin duniya ta gabatar. A maimakon haka sun buƙaci babban sakataren majlisar ta ɗinkin duniya Ban ki Moon daya jagoranci kwamitin binciken.

Wannan bukata da Palasɗinawan tare da ƙwayen su suka gabatar wa wakilan majalisar kare haƙƙin bil'adama ta MDD yazo ne a daidai lokacin da 'yan kwamitin ke fara wata mahawara akan daftarin rahoton da ake taƙadama akai, wanda ke zargin Israila da ƙungiyoyin Palasɗinawa masu ɗauke da makamai da aikata laifuna yaƙi daya haddasa hasarar rayukan Palasdinawa 1400 da kuma yahudawa 13. a faɗan Disemba zuwa janairu na wannan shekara.

Ko'a zaman da kwamitin sulhu majalisar ta ɗinkin duniyan ya gudanar jiya laraba a birnin New York ya Amirka, su kansu ƙawayen na Israila, irin su Amirka da Birtaniya da Faransa sun goyi da bayan buƙatar Israilan data ƙaddamar da binciken sojojin nata da rahoton kwamitin Richard Goldstone ya zarga da aikata laifukan yaƙi a lokacin yaƙin na Gaza.

Sai dai kuma kamar yadda ta saba Israila ta hannun jakadar ta a majalisar ta ɗinkin duniya Gabriela Shalev tayi watsi da rahoton ne ɗungurun gun, tare da baiya shi a matsayin na son kai da kuma nuna fifi ko ga wani ɓangare,ko kuma goyon bayan ta'addanci. Shalev ta ƙara da cewa:

" naji takaicin bayyana maku cewar wannan rahoto na Goldstone cike yake da son kai, kuma baya bisa turba, kuma ya kaucewa manufofin kafa shi. Rahoton ya goyi bayan aiyukan ta'addanci. kuma tamkar sakaiya ne ga ƙungiyoyin yan ta'adda. ya hana Israilan damar kare al'umar ta. A taƙaice ya faɗa tarkon kungiyoyin ta'addanci na duniya. kuma yan iya hana ƙasshe masu bin tafarkin demokiradiyya kare kansu daga aiyukan 'yan ta'adda akan su".

Amirka dai ta kasance babbar ƙawar Israilan a duniya, amma kuma kamar yadda aka sani manufofin sabuwar gwamnabtin Amirkan akan Isarailan ya sha babban dana tsohuwar gwamnatin ƙasar, kuma duk da cewar Amirkan har yanzu tana adawa da matakan tofin Allah tsine da Israilan.

Sai dai a ta bakin mataimakin jakadan Amirka a MDD Alenjandro Wolff, washington ta damu mataƙa game da sakamakon rahoton, musanman yadda rahoton ya maida hankali, akan Israilan, amma duk da haka fatan Amirka shi ne, ita ma Israilan ta duba wannan zargi da ake mata da idon basira.

" Akwai bukatar Isarila ta dakatar da shirin ta na gina matsugunai tare da kau da cibiyoyin bincike. Kuma Amirka bata goyon bayan cigaba da mamayewar yankunan Larabawa. Kuma akwai bukatar Israilan ta hinmatu wajen inganta shige da fice tare da haɓaka tattalin arzikin yankin yanmancin gaɓan kogin jordan. Su kuma palasɗinawa a nasu ɓagaren su inganta tsaro da garambawul ga gwamnatin su tare kuma da dakatar da tada tarzoma. Muna fatan dukkanin ɓagarorin, ciki kuwa harda sauran ƙasashen larabawa zasu zabura waje komawa teburin sulhu cikin hanzari".

Yanzu dai a yayin da ake ci gaba da wannan kace nace, rahonton na Richard Goldstone ya buƙaci a gabatar da zarge-zargen a gaban kotun hukunta masu aikata laifukan yaƙi na ƙasa da ƙasa dake birnin Hague, muddin Israilan da kuma Palasɗinawa suka ƙi ɗaukan matakan gudanar da bincike akan waɗannan laifukan.

Mawallafi: Jibril Babangida

Edita: Ahmad Tijani Lawal