Rahoton Cutar Aids a Zimbabwe da Afrika ta Kudu | Labarai | DW | 30.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rahoton Cutar Aids a Zimbabwe da Afrika ta Kudu

Gobe ne idan Allah ya kai mu, a ke bikin yaki da cutar kanjamau a fadin dunia baki daya.

A jajibirin wannan biki, gwamnatoci daban daban, na bayyana yanayin cutar ta AIDS a kasashen su.

A rahoton da ta hido, gwamnatin kasar ta kudu, ta yi nuni da cewa, cutar Sida ta jawo nakasar harakokin cigaban kasar fiye da kima.

Rahoton yace, sassan ma´adanai, makamashi, da suhuri, na daga wanda su ka fi galabaita da illolin cutar.

A jimilce, Afrika ta kudu, na daga sahun kasashen dunia da su ka yi fice ta fannin kamuwa da cutar Kanjamaw.

Mutane million 6 da rabi, ke fama da ita, inji rahoton hukumar opishin ministan kiwon lahia.

A cen kuwa Zimbabwe, mutane fiye da million daya da rabi, ke dauke da kwayoyin cutar kabari sallama alaikum.

Daga kussan jimmilar mutane dubu dari 2 da 80 , da a ka tabatar su na dauke da cutar kashi 7 kaccal ne bisa 100,ke samun tallafin manganin rage raddadin ta.