Rahoton cin hanci a duniya | Siyasa | DW | 26.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rahoton cin hanci a duniya

Har yau matsalar cin hanci na ci gaba da zama karantsaye ga harkokin ci gaba da ta da komaɗar tattalin arzikin ƙasashe masu tasowa

default

Tutar ƙungiyar yaƙi da cin hanci ta Transparency International

Ƙungiyar dake ƙoƙarin yaƙi da cin hanci da karɓar rashawa tsakanin ƙasashen duniya, wato "Transparancy International" a turance, ta fitar da rahoton ta na shekara ta 2010. Rahoton dai ya nuna gazawar ƙasashe da dama wajen kawar da wannan mummunar al'ada dake kawo naƙasu a fannoni rayuwa daban-daban.

A cikin rahoton da ƙungiyar ta fitar ranar talatan nan, ta bayyana ƙasashen da suka fuskanci matsalolin tattalin arziki irin su : Amurka, Girka, Italia da Hungary da cewa an samu ƙaruwar aikata cin hanci a cikin su. To amma duk da haka ƙungiyar ta Transparancy International, tayi kira ga mambobin ƙungiyar G20 masu ƙarfin masana'antu a duniya, da suyi ƙoƙarin yaƙar talauci, a yanzu da ake farfaɗowa daga matsalolin tattalin arzikin da duniya ta sha fama da shi.

Bugu da ƙari kuma, shugabar ƙungiyar Huguette Labelle, ta yabawa ya'yan ƙungiyar ta G20, bisa ƙudirin su na yaƙi da cin hanci gabanin taron da zasu gudanar cikin watan Nuwamba a birnin Seoul. Ƙasashen Denmark, New Zealand da Singapore ne ke kan gaba wajen ƙarancin karɓar cin hanci, inda Iraq, Afghanistan, Myammar da Somalia kuma ke kan gaba wajen badaƙalar karɓar cin hanci da rashawa a duniya baki ɗaya.

Dangane da nahiyar Afirka kuwa, rahoton ya nuna cewa ana ci gaba da samun ƙaruwar cin hanci, maimakon raguwa, duk kuwa da irin rajin da ƙasashen ke yi na cewa suna yunƙurin kawar da wannan mummunar ta'ada. Ƙasar Niger ta samu matsawa gaba ne daga matsayi na 106 a shekara ta 2009 zuwa na 123 a yanzu, Nigeria na a matsayi na 130 a bara, yanzu kuma 134 inda ƙasar Cameroun kuma ta ci gaba da riƙe matsayin ta na 146 kamar bara. Matsalar ta cin hanci, matsala ce da tayi tsamari daidai da irin ta canje-canjen yanayi da yaƙar talauci a ƙasashe masu tasowa, a cewar Edda Müller, shugabar ƙungiyar Transparency reshen Jamus. Matsalolin cin hanci kan hana ruwa gudu ga muhimman shirye-shiryen taimakon raya ƙasa da ake bayarwa:

Ta ce:"Wajibi ne a taron da za a gudanar a Cacun akan matsalar yanayi a kuma mayar da hankali ga matakan gyara ga al'amuran shugabanci a waɗannan ƙasashe da kuma wasu sabbin matakai na taimakon da suka cancanta akan manufa."

Ƙasar Jamus, dai ta ci gaba da zama a mataki na 15 kamar a shekarar da ta wuce, Birtaniya kuma daga 17 zuwa 20, Faransa 24-25 inda Amirka kuma ta tashi daga matsayi na 19- 22 cikin wannan shekarar. Edda Müller ta ƙara da bayani da cewar:

Ta ce:"Dalilin da ya sanya Jamus ta ci gaba akan matsayinta na bara shi ne kasancewar ƙasar ba ta rattaɓa hannu kan yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya akan cin hanci ba. Ana samun cikas akan haka ne sakamakon rashin cimma daidaituwa tsakanin gwamnati da majalisar dokoki, akan sakin layi na 108 na dokar hukunta miyagun laifuka a ƙasar, wadda ta shafi cin hanci daga ɓangaren wakilan majalisar dokokin ƙasar."

Wannan badaƙala ta cin hanci na ci gaba da zama ruwan dare tsakanin ƙasashe, inda ita kuma ƙungiyar ta Transparancy International ke kallon sa, a matsayin cin amanar da aka danƙa wa mutum domin cimma wasu burika na ƙashin kansa, hakan kuwa yana tattare abubuwan dake faruwa a ɓangarorin gwamnati da masu zaman kansu. A ko wacce shekara ƙungiyar na gudanar da binciken ta ne, kana ta bawa ko wacce ƙasa matsayi bisa matakin cin hancin dake akwai tsakanin shuwagabannin ta.

Mawallafi: Tukur Garba Arab

Edita: Ahmad Tijani Lawal

Sauti da bidiyo akan labarin