Rahoton binciken rikice rikicen makamai a duniya | Siyasa | DW | 18.10.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rahoton binciken rikice rikicen makamai a duniya

An samu matukar raguwar yake yake da mace mace a duniya,koma bayan yadda wasu mutane suke zato.

komitin sulhu na majalisar dinkin duniya

komitin sulhu na majalisar dinkin duniya

Binciken ,wanda gwamnatocin Canada,Norway,Sweden Switzerland da Burtaniya suka dauki nauyinsa, yace, yawan rikici da makamai ya ragu matuka da kashi 40 cikin dari tun daga 1992,hakazalika yawan kashe kashe cikin irin wadannan rikice rikice sun ragu da kashi 80 cikin dari.

Rahoton yace yawan juyin mulkin soji da yunkurin juyin mulkin na soji sun agu da kashi 60 tun 1963,inda aka samu juyin mulki ko yunkurin hakan sau 25, a 2004 kuma an samu yunkurin juyin mulki sau 10 wadanda dukkanninsu suka ci tura.

Kasashen Burtaniya,Faransa,Amurka da Rasha sune kasashen da suka yaki yawancin yake yake na duniya baki daya.

Kodayake rahoton yace,a yanzu yawancin yake yaken suna faruwa a mafi yawa ba kasashe matalauta na nahiyar Afrika.

Yawancin hasarar rayuka da ake samu kuma, inji rahoton,su kan faru ne sakamakon cututtuka da rashin abinci da yaki ke haddasawa,wanda a cewarsa ya kan kai kashi 90 cikin dari na yawan mace mace da ke da alaka da yake yake.

Duk da cewa an samu raguwar hasarar rayuka sakamakon yake yake,har yanzu akwai rikice rikice na makamai guda 60 a cikin duniya baki daya,hakazalika akwai batutuwa da dama na take hakkin bil adama,laifukan yaki da aiyukan taadanci a cewara rahoton.

Darektan wannan bincike,farfesa Andrew Mack,yace ba wata kungiya ta kasa da kasa da take tara bayanai akan yake yake ko aiyukan taadanci da take hakkin bil adama,wanda yace hakan ya sanya baa samun cikakken rahoto ko bayanai game da yake yaken,hakazalika yace, kafofin yada labarai sun fi maiada hankulansu akan sabbin rikice rikice da ke bullowa,maimakon wadanda aka kawo karshen su.

Rahoton yace,akwai kwararn dalilan siyasa uku da suka sanya aka samu raguwar yake yake da mace mace sakamakonsu,

Na farko,inji rahoton shine kawo karshen mulkin mallaka,inda yace, tun daga shekarun 1950 zuwa farkon shekarun 1980,yake yake da suka jibinci mulkin mallaka suke da kashi 60 zuwa kashi 100 bisa dari na dukkan rikice rikice na duniya,inda yace a yanzu ba irin wadannan rikice rikice.

Na biyu kuma, shine karshen yakin cacar baka tsakanin Amurka da tsohuwar taraiyar soviet wadda ita ta maye gurbin kashi daya bisa uku na dukkan tashe tashen hankula da suka biyu yakin duniya na biyu.

Rahoton yace,kawo karshen yakin cacar baka tsakanin wadannan manyan kasashe,ya kuma kawo karshen yake yake da suke haddasawa a tsakanin kasashe masu tasowa.

Dalili na uku kuwa,kamara yadda binciken ya baiayana,yunkuri na kungiyoyin dabam dabam a duniya na ganin an kawo karshen,yake yake da kare abkuwar su tare da kula da kare hakkin bil adama.

Wani abu kuma a cewar rahoton shine aiyukan kiyaye zaman lafiya na Majalisar dinkin duniya tare da takunkumi da take dorawa kasahe da suke da taurin kai.

A halin yanzu,majalisar dinkin duniya tana gudanar da aiyukan wanzar da zaman lafiya 16,da kusan dakarunta dubu 17 da suke kasashe kama daga Lebanon zuwa Georgia,daga Haiti zuwa Saliyo suna aiyukan wanzar da zaman lafiya.

Binciken yace kodayake ba Majalisar dinkin duniya ba kadai take kokari na ganin an samu zaman lafiya a duniya,bankin duniya da dubban kungiyoyi na kasa da kasa suma suna taka muhimmiyar rawa a nasu bangare, sai dai yace majalisar dinkin duniya wadda da ke da cikakken iko,ce kadai take kan gaba a aiyukan wanzar da zaman lafiya.

Da yake baiyana dalilan da suka sanya aka samu raguwar yake yake,rahoton yace a baya anyi anfani da manaya makamai,da kuma tsoma baki na wasu kasashe,hakazalika yace da yawan yan gudun hijira da suke tserewa tashe tashen hankula,wanda ahoton yace ba din haka ba da an halaka jamaa da dama a wadannan yankunan.

Amma,rahoton yace,kada ganin cewa ana kara samun wanzuwar zaman lafiya a duniya,hakan ba wani batu ne da farin ciki ga jamaarda da yanzu suke cikin wahala a Darfur,Iraqi,Kolombia Nepal da jamhuriyar demokradiyar Kongo ba.

 • Kwanan wata 18.10.2005
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu4q
 • Kwanan wata 18.10.2005
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu4q