Rahoton Bankin Duniya Akan Cin Hanci | Siyasa | DW | 14.05.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rahoton Bankin Duniya Akan Cin Hanci

Tsaffin kasashen kwaminis na gabacin Turai sun samu kyakkyawan ci gaba a fannin siyasa da tattalin arziki a cikin shekarun baya-bayan nan

Shelkwatar Bankin Duniya a Washington

Shelkwatar Bankin Duniya a Washington

Duk da wannan kyakkyawan ci gaba matsalar cin hancin tana ci gaba da addabar wadannan kasashe tare da hana ruwa gudu wajen zuba jarin kamfanonin ketare a cikinsu. Wasu kamfanonin da aka nemi jin albarkacin bakinsu a game da ayyukansu a kasashen Krowashiya da Azerbaijan da Kasachstan da Kirgistan da Lituaniya da kuma Rasha sun nuna cewar matsalar cin hanci tayi sauki a shekara ta 2002 idan aka kwatanta lamarin da shekarar 1999. Amma babu wani sauyin da aka samu dangane da kasashen Bosniya-Herzegovina da Bulgariya da Macedoniya da Georgiya da Rumeniya da Ukraine da kuma Slovakiya. Dangane da kasashen Poland da Bailorushiya kuwa matslar cin hanci ta karu ne fiye da kima. A takaice dukkan kasashen na gabacin Turai har yau suna fama da tabargazar karbar rashawa da hanci ko kuma abin da su kan kira wai tukwici akan hidimomin da suka gabatar wa mutum, kamar yadda aka ji daga Sheryl Gry daga Bankin Duniya. Ya kuma kara da cewar:

Ko da yake an samu kyakkyawan ci gaba a wasu tsaffin yankunan rusasshiyar Tarayyar Soviet, musamman wadanda suka shigo inuwar Kungiyar Tarayyar Turai, amma kasa kamar Poland har yau tana fama da wannan kayar kifi a wuyanta. A cikin shekarun baya-bayan nan dai kasar ta tashi haikan wajen shawo kan matsalar, kuma ba shakka Bankin Duniya zai ba da sakamakon wannan kokari nata a cikin rahotonsa na gaba. A hakikanin gaskiya dai matsalar ta hanci ta dada kazancewa a Poland tsakanin 1999 da shekara ta 2002.

Bayanai sun nuna cewar a shekara ta 2002, ko da yake an samu raguwar hanci a kasashe tara daga cikin kasashe 24 na gabacin Turai, amma a daya bangaren an samu bunkasar yawan kudaden hancin. Kasashen Kirgistan da Albaniya sune akan gaba, inda yawan kudaden hancin ya kan kama kashi 3-4% na jumullar kudaden shiga na kamfanin da lamarin ya shafa. A da yawa daga cikin kasashen da suka shigo inuwar KTT adadin ya gaza na kashi 1%. Kazalika kananan kamfanoni na cikin gida sun fi jin radadin lamarin akan manyan kamfanoni na kasa da kasa. Bisa ga ra’ayin Bankin Duniya dai matsalar hanci ba wata annoba ce daga Indallahi ba, abu ne da za a iya magance shi idan an yi niyyar yin hakan tsakani da Allah. Grey ya kara da cewar:

Maganar ba kawai ta shafi tsare wasu jami’ai ‚yan kalilan ne a kurkuku ba, muhimmin abu shi ne a gabatar da nagartattun matakai na garambawul da kuma raba alhaki daidai wa daida tsakanin dukkan kafofi na gwamnati. Wajibi ne a tantance karfin ikon kowace kafa da kuma ba wa daidaikun mutane da kafofin yada labarai cikakken ‚yancin fadin albarkacin bakinsu akan kurakurai na gwamnati.

Wani kuma abin da zai taimaka wajen yaki da cin hanci shi ne mayar da kamfanonin gwamnati ga ‚yan kasuwa masu zaman kansu da hana babakeren wani kamfani daya a ayyukan samarwa. To sai dai kuma rahoton na Bankin Duniya ya kara da nuna yadda su kansu kamfanonin ke cike gibinsu na kudaden hanci da suke bayarwa ta hanyar kazamar ribar da suke ci akan kayayyakinsu.