Rahoton Bankin Dunia a game da tattalin arzikin Afirika | Siyasa | DW | 14.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rahoton Bankin Dunia a game da tattalin arzikin Afirika

bankin Dunia ta ƙaddamr da rahoto a game da yanayin ci gaban Afirika a tsawan shekaru 10 da su ka gabata.

default

Rahoton Bankin Dunia a game da ci gaban Afirika

Ranar 14 ga watan Nowemba na wannan shekara, Bankin Dunia, ta gabatar sakamakon wani bincike, da ta gudanar,domin tantance ci gaba ko kuma koma bayan da aka samu a nahiyar Afrika, ta fannin tattalin arziki, da kyauttata rayuwar jama´a, a tsawan shekaru 10, wato daga shekara ta 195 zuwa 2005.

A cikin wannan rahoto Bankin Dunia,ta gano cewar ƙasashe da dama na Afrika ,sun sami ci gaba mai inganci idan aka kwatata da taɓarɓarewar al´ammura a nahiyar, daga shekara ta 1975 zuwa 1985, sannan a n samu ci gaba idan aka awana da matsayin babu yabo babu fallassa da Afrika ta sami kanta a ciki, daga 1985 zuwa 1995.

Saidai rahoton ya karkasa ƙasashen Afrika a rukunai guda 3, akwai wanda su ka sami ci gaba na zahiri, da wanda su ka ɗan cira, sai kuma rukunin yan koma baya, wanda har yanzu jama´a ke fama da ƙazamin talauci a cikin su.

A cewar John Page shugaban sashen tattalin arziki a reshen Afirika na Bankin Dunia , a tsawan shekaru 10 da su ka wuce Afirika ta sami ci gaba na kashi 5,4 cikin100.

John Page ya ci gaba da cewa:

„Tun shekara ta 1995, mun gano cewar akwai wani abu da ke cenzawa a Afrika.

Dalilai guda 3 su ka tabbatar mana da hakan:

Na farko dai Afirika ta sami kutsawa a ƙasashen dunia, inda ake damawa da ita, ta fannonin siyasa, diplomatia da cinikaya, sannan kampanoni masu zaman kansu, sun bunƙasa, kazalika tattalin arzikin nahiyar baki ɗayan sa, ya fara komawa a kan turba ta gari“.

Duk da cewar babu kampanoni masu ƙarfi mallakar Afrika amma wasu ƙasashen nahiyar sun cencenci yabo ta fannin saye da sayarwa da ƙetare inji rahoton na Bankin Dunia.

Ƙasashe 34, su ka yi nasara bunƙasa hajojin da su ke saidawa ƙetare tsakanin shekara ta 2004 zuwa 2005 daga dala milion dubu 182, zuwa dalla milion dubu 230.

A wannan ɓangare ƙasashen Ruanda, Lesohto, Kenya Madagascar sun ciri tuta.

To saidai kamar yadda wannan rahoto ya nunar, ci gaban ya bambamta daga wannan ƙasa zuwa wacen, alali misali a Zimbabwe, ana matsayin ko war tuna bara bai ji daɗin bana ba , ta la´kari da mummunan koma bayan da ƙasar ta samu, idan a ka kwatanta da rahoton shekara ta 1985 zuwa 1995.

A tsawan shekaru 10, baya Zimbabwe ta sami koma baya na kasa ga kashi 2 cikin 100.

Wannan matsayi ya saɓawa ƙasar Equatorial Guinea wada ta samu ci gaba na kashi kussa 31 cikin 100, kuma ita ce jagora, a sahun ƙasashen da su ka taka rawar gani, a game da ta talauci a nahiyar Afrika.

Rukunin farko na ƙasashe 8 da su ka fi samin ci gaba, mafi yawan su sun haɗa da ƙasashen da su ka mallaki albarkatun man Petur kamar Taraya Nigeria, Equatorial Guinea da Uganda.

Sannan rukuni na 2 ya ƙunshi ƙasashe 18, rukunin ƙarshe na ƙasashen da a su taɓuka komai ba, ya ƙunshi mafi yawan ƙasashen yanki Afrika ta Kudu ga Sahara.

Kamar yadda wannan rahoto ya nuna Afrika na fuskantar kwan gaba kwan baya, wajen ci gaba, Jorge Saba Arbache masani ta fannin tattalin arziki ya kuma bayana wasu daga dalilan wannan matasyi na Afrika.

„ zan iya bayyana 3 daga cikin wannan dalilai, na farko dai shine yaƙe-yaƙe, ƙanana da manya, da wasu ƙasashen Afirika ke fama da su, wanda kuma ke hadasa babban koma baya, sai kuma gudanar da harakokin mulki, ayyukan da mu ka yi tare da hukumomin ƙasashen dabam-dabam, sun nunar mana cewa,r salon mulki ya bambamta daga wannan shugaba zuwa wancen,sannan da dama daga ƙasashen Afirika, sun yi dogaro ne a kan wasu hajoji, wanda su ke saidawa a ƙetare, alal misali,wasu sun yi dogaro da man petur wasu da albarkatun noma, ko kuma wasu sauran albarkatu na ƙarƙashin ƙasa.

Saboda haka, a duk lokacin da parashen wannan hajoji ya tashi a kasuwanin dunia, to ƙasashen kan samu riba mai tsoka, a yayin da kuma idan parashen ya faɗi, sai su shiga wani mayuwacin hali, domin basu da wata madogara ta dabam“.

Ƙarin matsalolin da su ka hana sauran ƙasashen Afrika kai wa ga tudun dafawa sun hada da cin hanci da karɓar rashawa.

Domin kwance wannan dabaibaiyi da ke hana Afirika samun ci gaba mai ɗorewa, Bankin Dunia ta yi kira ga magabatan Afirika su himmantu, wajen raba hannuwa a game da batun saida hajoji a ƙetare,sannan su tabbatar da mulki na gari cikin adalici, wanda shine tushen yaƙi da talauci a dunia.