1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton ayyukan ta´addanci a duniya ya fito

September 27, 2006
https://p.dw.com/p/BuiE

Gwamnatin Shugaba Bush ta fitar da wani na rahoton dake kunshe da ayyukan ta´addanci a duniya. Rahotonni dai sun nunar da cewa kusan dukkannin hukumomi na leken asrin Amurka 16 ne suka shirya wannan rahoto.

Wasu sassan rahoton da a kwanan nan aka tseguntawa jaridar New york Times, sun nuna cewa hukumomin leken asirin Amurka nada ra´´ayin cewa yakin Iraqi ya taimaka wajen yadda Amurka ke kara fuskantar hare haren ta´addanci.

A waje daya kuma Shugaba Bush, ya ya zargi wadanda suka rubuta rahoton da cewa babu wata alaka, a tsakanin yakin na Iraqi da kuma batu na yadda ake kara samun yawaitar masu tsattsauran ra´ayi.

Bush yace.... zamu yi kokarin dakatar da wannan jita jitar dake na siyasa a cikin ta na fadin abin da bashi ke nan ba a game da Iraqi, domin kuwa kokari ne kawai akeyi na yawo da hankalin mutanen Amurka don kada su fuskanci ainihin abin da ke da akwai...

Bugu da kari shugaban na Amurka ya soki lamirin wannan rahoto, da jaridar New York Times ta buga wani bangare na cikin sa, da cewa anyi hakan ne don cimma wata manufa a game da harkokin zabe da ake shirin yi a watan nuwamba.