1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton Amurka aka hakkin dan-Adam

March 9, 2006

Kasar Amurka na zargin kasashen Rasha da China da IRan da Koriya ta Arewa da kuma Kuba da laifin keta haddin dan-Adam

https://p.dw.com/p/Bu1D

A lokacin da take gabatar da kundin rahoton na shekara, sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice cewa tayi: ‘Yanci da Walwala da Mulki na demokradiyya sune shika-shikan mutuncin dan-Adam. Bisa al’ada dai rahoton na gwamnatin Amurka akan hakkin dan-Adam ya kan duba dukkan kasashe 196 ne dake da wakilci a MDD. Amma tun a babin gabatarwa na rahoton aka kebe wasu kasashe biyar, wadanda aka ce sune akan gaba wajen take hakkin dan-Adam a duniya. Wadannan kasashe kuwa sun hada ne da Koriya ta Arewa da Burma da Iran da Zimbabwe da Cuba da kuma China. Kazalika rahoton ya kalubalanci wasu kasashen larabawa dake kawance da Amurkan. Misali rahoton ya zargi kasar Masar da azabtar da fursinoni, a yayinda ita kuma Saudiyya ake zarginta da kame-kamen fursinoni ba gaira ba dalili. Dangane da Iraki da Afghanistan kuwa al’amura na dada tabarbarewa ne sakamakon mawuyacin hali na tashe-tashen hankula da kasashen ke ciki. Condoleeza Rice ta kara da cewar:

“Dukkan dan-Adam, maza da mata dake doron duniyar nan tamu na da cikakken hakkin rayuwa a cikin mutunci da walwala. Cika kudurorin kare hakkin dan-Adam na MDD da kuma gina sahihin tsari na demokradiyya a duk fadin duniya shi ne babban abin da aka sa gaba tun shekaru aru-aru da suka wuce, kuma wannan manufa ce da wajibi ne a tabbatar da ita, amma ba a ci gaba da yin watsi da ita ba.”

Rahoton yayi bayani akan dangantakar dake akwai tsakanin mulki na demokradiyya da girmama hakkin dan-Adam. Amma fa gudanar da zabe na demokradiyya kawai ba ya ma’anar girmama hakkin dan-Adam. Kasashe masu mulki na danniya da kama kariya suna barazana ga zaman lafiyar duniya, a cewar rahoton, wanda ya ambaci kasar Iran. Sai dai kuma rahoton bai tabo maganar hali da ake ciki dangane da hakkin dan-Adam a ita kanta Amurka ba, ko da yake Laryy Lowenkron, karamin minista a ma’aikatar harkokin wajen Amurkan ya ce wannan batu ne da za a iya tattaunawa kansa. Amma yayi fatali da korafin da ake yi, musamman daga bangaren majalisar dinkin duniya a game da sansanin gwale-gwalen nan na Amurka, inda yake cewar:

Gwantanamo sansani ne dake karkashin kudurin kare hakkin dan-Adam na kasa da kasa da kuma dokoki na yaki. Mun ji takaici kwarai a game da cewar masu alhakin rubuta rahoton MDD ko yunkurin kai ziyara sansanin ba su yi ba ballantana su yi musayar yawu da likitocin dake wurin. Rahoton nasu ya dogara ne akan abubuwan da lauyoyin fursinonin suka fada musu.