1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton Amnisty a game da yankin Darfur

June 29, 2006
https://p.dw.com/p/BusL

Hukumar kare haƙƙokin bani Adama ta ƙasa da ƙasa, Amnisty International, ta yi kira ga ƙasashen dunia, da su ɗauki matakan ceton rayukan dubbunnan jama´a fara hulla, da ke zaune a gabacin ƙasar Tchad, a karbun iyaka da Sudan.

Wannan kira, ya biwo bayan hare haren da al´umomin yankin ke fuskanta daga yan Djandjawid na ƙasar Sudan.

Mutane a ƙalla dubu 765, su ka ƙauracewa matsugunnan su, dalili da wannan hare hare inji Amnisty International.

Sakatare Jannar na wannan hukuma, Irene Khan, ya zargi gwamnatin ƙasar Tchad, da mantawa kwata-kwata, da al´ummomin ƙasar da ke zaune a iyaka da Sudan.

Irene Khan, ya yi kira na mussamman, zuwa ga shugabanin ƙasashen Afrika da za su zaman taro a ƙarshen wannan mako, a birnin Banjul na ƙasar Gambia,da su dubi wannan matsala da idon basira, su kuma samar mata maganin da ya dace.

Sannan hukumar Amnisty, ta buƙaci shugabanin na Afrika, su mayar da Sudan saniyar ware, a dalili da adawar da ta ke, a kan batun tura dakarun Majalisar Ɗinkin Dunia zuwa yankin Darfur.