Rahoton Amnesty A Kan Halin Da Ake Ciki A Darfur | Siyasa | DW | 21.09.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rahoton Amnesty A Kan Halin Da Ake Ciki A Darfur

Kungiyar neman afuwa ta Amnesty tayi kira ga MDD da ta kara matsin kaimi akan gwamnatin Sudan domin shawo kan rikicin lardin Darfur da ya ki ci ya ki cinyewa tare da ba da damar kai taimakon jinkai ga 'yan gudun hijirar da suka tagayyara a wannan yanki

Mata dauke da kiraren wuta a lardin Darfur

Mata dauke da kiraren wuta a lardin Darfur

A farkon wannan makon an saurara daga bakin ministan kula da hakkin dan-Adam na kasar Sudan Ibrahim Mahmoud Hamed yana mai bayanin cewar gwamnatinsa tayi alkawarin tabbatar da tsaro da share hanyar taimakon jinkai a lardin Darfur. A sakamakon haka gwamnatin Sudan ta mayar da martani da kakkausan harshe akan barazanar da MDD tayi na kakaba wa kasar takunkumi akan masana’antunta na mai. A lokacin da yake bayani game da haka Ibrahim Mahmoud Hamed cewa yayi:

Muna bakin kokarinmu, saboda a wuyanmu ne alhakin kyautata makomar al’umar kasar nan ya rataya. Muna kira ga dukkan masu korafi da su ba mu hadin kai domin samun bakin zaren warware matsalar. Amma ci gaba da Tofin Allah Tsine akan gwamnatin Sudan ba zai tsinana kome ba.

MDD da sauran kungiyoyi na kasa da kasa sun bayyana matukar damuwarsu a game da fadan da ake ci gaba da fafatawa a Darfur da kuma mawuyacin hali da sauran talakawa ke ciki a Darfur. A makon da ya gabata taron sulhu tsakanin wakilan gwamnati da na ‚yan tawayen Darfur ya watse ba tare da an cimma tudun dafawa ba. Gwamnati a fadar mulki ta Khartoum ta bayyana wa tawagar wakilan Amnesty da ta kai ziyarar bin bahasi a lardin Darfur bacin ranta a game da kudurin baya-bayan nan na MDD, wanda take gani tamkar rashin adalci ne daga bangaren majalisar. Amma duk da haka ta ce zata yi biyayya ga wannan kuduri. Da yawa daga wakilan gwamnatin dai sun ce ba su ne ke da alhakin ta’asar keta haddin dan-Adam dake faruwa a Darfur ba, amma fa har ya zuwa halin da muke ciki yanzu Larabawa ‚yan janjaweed na ci gaba da cin karensu babu ba babbaka, inda suke kashe-kashe na gilla da fyade da kone-konen gidaje da kadarorin mutane ba gaira ba dalili. Kazalika har yau dubban mutane na ci gaba da gudun hijira a cewar Irene Khan, babbar sakatariyar kungiyar Amnesty. A wannan marra da ake ciki yanzun ba a hangen lokacin da wannan rikici zai kawo karshensa saboda tuni akan bannatar da madogarar rayuwar dubban daruruwan mutane a lardin. Kungiyar ta Amnesty ta ce ta bayyana wa fadar mulki ta Khartoum muhimmancin daukar matakai na gaggawa domin tsaron lafiyar ‚yan gudun hijirar a ciki da kuma wajen sansanoninsu. Kazalika kungiyar tayi kira da a ba wa kungiyoyin taimako na kasa da kasa cikakkiyar damar kai taimakon jinkai ga wadannan mutanen dake cikin hali na zautuwa ita kuma MDD wajibi ne ta ci gaba da matsin lamba akan fadar gwamnati ta Khartoum domin shawo kan wannan rikici.