Rahoton 2009 na ƙungiyar kare hakƙin bil Adama ta Duniya | Siyasa | DW | 14.01.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rahoton 2009 na ƙungiyar kare hakƙin bil Adama ta Duniya

Kungiyar Human Rights Watch ta zargi ƙasashe da dama da tauye haƙƙin bil Adama

default

Tambarin Ƙungiyar Human Rights Watch

Rahoton na bana da Hukumar Kare hakkin Bil'adaman dake da Hedikwata a Birinin New York ta kasar Amurka ta bayar yana kunshe ne a kundi mai shafi 564.Kuma kamar kowace shekara kasashe da dama kama daga Amurka da Turai da kuma uwa-uba kasashen Asia da Afrika, basu tsira ba daga zargezage daban daban dake da nasaba da gallazawa da kuma cin zarafi ko karya yancin Bil'adama.

Rahoton daya fi daukan hankali a kasashen Afrika dai,shine wanda aka wallafa akan kasashe irin su Najeriya da Zimbabwe da Masar da Chadi da sudan da kuma Rwanda.

Rahoton da kungiyar ta HRW ta fitar dai akan Najeriya,ya zargi gwamnatin Umaru Musa Yar'adua data shafe shekaru biyu cur akan karagar mulki ne da gazawa wajen magance matsalolin karya hakkin bil'adama a kasar duk kuwa da dunbin kudaden da take samu na cinikin man fetur a shekarar data gabata.Kungiyar taji takaicin yadda cin hanci da rashawa ya hana yan najeriyan samun ingantacciyar lafiya da kuma ilimi.

Kungiyar ta HRW ta baiyana sauya shugaban Hukumar yaki da cin hanci da rashawa Nuhu Ribado da gwamnatin Najeriya tayi da cewar ya maida hannun agogo baya wajen kawar da wannan annoba.

Sauran Batutuwa da Kungiyar ta tabo,sun hada da watsi da Dokar baiwa yan jarida samun bayanai na gwamnati da rikicin yankin Niger Delta da kuma rikicin addini da kabilanci a Jihar Plato datace ya lakume rayukan jama'a da yawan su ya haura Dubu Goma Sha biyu da kuma matakin ba sani ba sabo da Hukumomi suka dauka akan wasu kafofin yada labarai tare da kamawa da kuma tsare wasu Yan Jaridu akan aiyukan su na yau da kullum.

Haka kuma rahoton yayi tsokaci akan tsarin Shrai'ar musulunci a wasu jihohin Arewacin Najeriya 12.

Amma kuma kungiyar taji takaicin yadda kasashen Duniya musanman Amurka da Burtaniya dake cin gajiyar dimbin arzikin man fetur da Najeriya kedashi suka kasa taka mata birki akan irin wayannan aika-aikan.

Game da zargin da akewa kasar Zimbabwe da laifin karya Hakkin Bil'ada kuwa, jami'ar Kungiyar ta HRW dake nan jamus Marianne Heuwagen tace"Muna fatan samun hadin kai tsakanin kasashen dake makwabtaka da zimbabwe a lemar kungiyar kasashen kudancin Afrika na ganin sun tashi tsaye akan Mugabe domin kawo karshen kangin daya sanyawa jama'ar Kasar sa.Ko kadan bamu ji dadin matakin da gwamnatin data gabata a kasar Afrika ta kudu ta dauka ba,musanman tsohon shugaban kasar Thabo Mbekei ya dauka ba.Amma a yanzu muna fatan za'a dauki matakan da suka dace domin magance wayannan matsaloli"

Da kungiyar ta HRW ta koma kan kasashen Turai da Amurka kuwa ,tayi abin nan da ake cewa Tsumangiyar kan hanya, inda ta zargi kasashen na Turai da daukan matakan da suka sabawa Dokokin Duniya wajen yaki da ta'addancin dana yan gudun Hijrah ko bakin haure.

Don haka kungiyar tayi kira ga kasar faransa data yi gyara a Dokar nan data baiwa yan sanda tsare wanda ake zargi da aiyukan ta'addacin harna tsawon sa'oi 72 ba tare da ganin lauyan sa ba.A yayin da kungiyar ta zargi kasar jamus da nuna wariya akan masu neman mafaka musamman yan afrika.

Da kungiyar HRW ta juya kan kasar Amurka kuwa,tayi kakkausan suka ga Dokokin zartar da Hukuncin kisa akan masu laifi, inda tace tsakanin watan Mayu zuwa Oktoban shekarar data gabata kadai an kashe mutane 30 yawancin su a jihar Texas inda shugaba Bush ya fito, tare da zartar da Hukuncin Daurin rai da rai akan wasu 2500 da shekarun su bai haura 18 ba.

A karshe Kungiyar tayi fatan sabon shugaban Amurka Barak obama zai hanzarta rufe gidan yarin nan na Guantanamo Bay dake kasar Cuba kamar yadda yayi alkawari ,wanda Sojojin Amurkan ke anfani dashi wajen yin gwalegwale ga wayan da ake zargin yan ta'adda ne a Duniya,wanda kungiyoyi kare hakkin bil'adama na cikin amurka da wajen ta dawasu kasashe ke ganin Ba karamin Karya ghakkin bil'ada akeyi ba a sansannin.