1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoto kan laifukan yaki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Gazali Abdou Tasawa
July 5, 2017

Kungiyar yaki da cin zarafin bil'adama ta kasa da kasa ta Human Rights Watch ta fitar a wannan laraba da wani rahoto kan laifukan yaki da mayakan kungiyoyin da ke yaki da juna a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya suka aikata.

https://p.dw.com/p/2fwK8
Zentralafrikanische Republik Militzionäre
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Delay

Kungiyar yaki da cin zarafin bil'adama ta kasa da kasa ta Human Rights Watch, ta fitar a wannan laraba da wani rahoto kan laifukan yaki da na cin zarafin bil adama da mayakan kungiyoyin da ke yaki da juna a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, suka aikata tsakanin shekara ta 2014 zuwa ta 2017. 

Rahoton ya bayyana cewa mayakan kungiyar Musulmi ta Seleka da kuma abokiyar gabarta ta Kiristoci ta Anti-Balaka, sun kashe fararan hula da tare da yi wa mata fyade, da kuma rusa kauyika masu yawa a lokacin fadan nasu. Rahoton ya zano kisan fararen hula 566 a cikin birane da wasu 144 a cikin yankunan karkara.

Kungiyar ta HRW za ta gabatar da wannan rahoto nata da ma wanda Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a watan Mayun da ya gabata, a gaban kotun musamman  ta CPS, wace aka kafa domin gurfanar da mutanen da suka aikata laifukan yaki a jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar tun daga shekara ta 2003. A ranar 30 ga watan Yunin da ya gabata ne dai aka rantsar da babban alkalin kotun ta CPS wacce za ta soma aiki a watan Oktoban wannan shekara ta 2017.