1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoto game da bunkasar jama´a a duniya

Mohammad Nasiru AwalSeptember 15, 2004

To rahoton game da bunkasar jama´a a duniya ya kunshi alkalumma ne wadanda ke yin nuni da irin ci-gaba ko kuma akasin haka da aka samu, tun bayan taron kasashen duniya game da bunkasar al´uma wanda ya gudana a birnin Alkahira kimanin shekaru 10 da suka wuce.

https://p.dw.com/p/BvgS

To rahoton game da bunkasar jama´a a duniya ya kunshi alkalumma ne wadanda ke yin nuni da irin ci-gaba ko kuma akasin haka da aka samu, tun bayan taron kasashen duniya game da bunkasar al´uma wanda ya gudana a birnin Alkahira kimanin shekaru 10 da suka wuce. Bettina Maas wakiliyar MDD ta ce ana kan hanyar da ta dace, domin tun bayan kaddamar da shirin tallafawa bunkasar jama´a a duniya a cikin shekarar 1994, halin rayuwar mutane a kasashe masu tasowa ya inganta, sannan sai ta kara da cewa.

"An samu nasarori iri dabam-dabam. Domin a halin da ake ciki yawan ma´aurata dake bin tsarin kayyade iyali ya karu da daga kashi 55 zuwa kashi 61 cikin 100, yayin da matsayin mata a kasashe masu tasowa da dama ya ingantu. Yanzu haka dai kasashe da dama sun kafa dokokin ba da kariya ga mata. Sai dai da sauran rina a kaba, musamman wajen aiwatar da wadanan dokoki. Amma duk da haka ana kan turbar da ta dace."

Manyan matsalolin da ake fuskanta wajen cimma manufar da aka sa gaba sun hada da yaduwar cutar AIDS ko Sida sai yawan mace-macen mata masu juna biyu, inji Renate Bähr ta gidauniyar tallafawa bunkasar jama´a a duniya ta nan Jamus.

"Sabanin bukatun da aka gabatar da su a cikin gagarumin shirin na birnin Alkahira, har yanzu ba´a samu wani ci-gaba na a zo a gani ba wajen rage yawan matan dake mutuwa a lokacin da suka zo haihuwa. Mata kimanin rabin milkiyan ke gamuwa da ajalinsu sakamakon matsaloli na ciki ko haihuwa."

Alalhakika kamata yayi a ce tuni an yi nisa, amma kamar a sauran shirye-shirye na MDD a nan din ma rashin isashen kudi na hana ruwa gudu bisa cimma burin da aka sa gaba. A wajen taron na birnin Alkahira kasashe masu ci-gaban masana´antu sun yi alkawarin ba da taimakon kudi na dakla miliyan dubu 6.1 a kowace shekara, amma a bara alal misali dala miliyan dubu 3 kadai suka bayar. Ita ma Jamus abin da take bayarwa yanzu bai kai yawan wanda ta yi alkawari da farko ba, inji Erich Stather karamin minista a ma´aikatar raya kasashe masu tasowa.

"Ba zamu iya cika dukkan alkawuran da muka dauka ba saboda dalilai na gibin kasafin kudi. Amma duk da haka muna iya kokarin sauke dukkan nauyin da suka rataya a wuyanmu."