1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahotanni kan Afrika a wannan makon

YAHAYA AHMEDJuly 22, 2005

Mafi yawan jaridun Jamus, sun fi mai da hankullansu ne kan bala'in yunwar da ake fama da ita a kasar Nijer. Jaridar Tageszeitung ce ta fi ba da cikakken rahoto a kan wannan annobar.

https://p.dw.com/p/Bvp9
Jaridar "die tageszeitung"
Jaridar "die tageszeitung"Hoto: npb

A cikin wannan makon, jaridun Jamus sun mai da hankalinsu game da Afirka ne, a kan bala’in yunwar nan da ake huskanta a kasar Nijer. Sai kuma wani sharhi da jaridar Süddeutsche Zeitung ta buga kan dalilan da suka janyo barkewar rikici a arewacin kasar Kenya, inda mutane 77 suka rasa rayukansu. Har ila yau dai, wasu jaridun kuma sun dubi irin halin da ake ciki yanzu ne a kasar Zimbabwe, bayan da shugaba Robert Mugabe ya ba da umarnin rusa matsugunan marasa galihu a unguwannin da ke wajen birnin Harare. Yunkurin da kasashen Afirka ke yi na samun zaunannun kujeru a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, shi ma ya sami ambato a cikin jaridun Jamus a wannan makon.
Bala’in yunwar da ake yi yanzu a kasar Nijer dai, ya kai innanaha. Haka ne jaridar Tageszeitung ta kwatanta irin halin da ake ciki yanzu a kasar ta Yammacin Afirka. A sharhin da ta buga kan wannan batun, jaridar ta ce, Nijer, kamar dai kasashe matalauta da dama na nahiyar Afirka, ba a buga labarai a kanta, sai dai in wani bala’i ya kunno kai. Abin kunya ne dai ga gamayyar kasa da kasa, inji jaridar, da yin sakaci da matsalar da Nijer din ke huskanta, har sai da aka kai lokacin da mutane suka fara sumewa da mutuwa, ana kuma nuna hotunansu a duk kafofin yada labaran duniya, kafin kasashe mawadatan su farga da abin da ke wakana, sa’annan su dau mataki.

Jaridar nan ta Süddeutsche Zeitung ta buga wani rahoto ne kan mummunan tashin hankalin nan da ya auku a makon da ya gabataa arewacin kasar Kenya, inda ta ce kusan mazauna kauyen Turbi 50 ne aka yi wa kisan gilla, sa‘annan wasu 27 kuma suka mutu daga baya. Jaridar ta kara da cewa:-

„Yara 20 na cikin wadanda aka kashen. Sai dai, saboda nisan kauyen daga birnin Nairobi, da kuma kasancewars a cikin karkara, jami’an ceto ba su samu sun kai gun da wuri ba. Rikicin dai ya barke ne, lokacin da wasu `yan daba na kabilar Borana, kimanin su dari biyu dauke da adduna da kulake da wasu makamai, suka afka wa kauyen na Turbi, inda ban da mutanen da suka rasa rayukansu, kusan 100 kuma suka ji rauni. „

Kafofin yada labaran kasar Kenyan, inji jaridar, sun ce `yan kauyen da aka yi wa kisan gillar sun fito ne daga kabilar nan ta Gabra, wadda wani reshe ne na kabilar Oromo ta kasar Habasha. Dalilin wannan rikicin dai shi ne, rigingimun da kabilun yankin ke yi kan filayen kiwo da na ban ruwa.

Jaridar Die Welt, ita ma ta yi sharhi kan wannan kisan gillar da aka yi a arewacin kasar Kenya, inda ta kiyasci cewa, kawo yanzu, kusan mutane 70 ne aka tabbattar sun rasa rayukansu. Jaridar dai ta ari bakin `yan majalisar kasar da dama ne suna sukar gwamnati da rashin daukan matakan da suka dace don hana aukuwar annobar. A ganin jaridar ta Die Welt dai, gwamnatin Kenyan ta yi watsi da wannan yannkin ne saboda ba shi cikin yankunan da masu yawon shakatawa ke ziyarta a kasar. Bugu da kari kuma, saboda yawan rikice-rikicen da ake samu a wannan yankin, sumogan makamai daga kasashe mabwabtan Kenyan kamarsu Sudan, da Habasha, da Somaliya, zuwa wannan yankin ba wani abu ne mai wuya ba.
Har ila yau dai, jaridar ta bayyana ra’ayin cewa, wasu `yan siyasa ma na da hannu a harin. Sau da yawa, inji Die Welt, `yan siyasan ne ke angaza `yan kablilunsu da su fatattaki tsirarun `yan wasu kabilun daban da ke zaune a wasu yankunna. Ta hakan, za su iya tabbatad da samun cikakken goyon baya da kuma rinjayin kuri’u a lokacin zabe.

Ita ko jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, ta buga rahoto kan Afirkan ne da ya shafi yunkurin da kungiyar Tarayyar Afirka, wato AU, ke yi na samun kujerun dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar dinkin Duniya.
Bisa cewarta dai, jakadun kasashen Afirka a Majalisar dinkin Duniyar, sun yi wani taro a ran larabar da ta wuce, inda suka zartad da kudurin mika bukatunsu ga taron koli na Majalisar. Aana dai kyautata zaton cewa, ministan harkokin wajen Najeriya, Olu Adeniji ne zai mika da kudurin yau juma’a ga taron.
Su dai kasashen Afirkan, inji jaridar, na bukatar samun kujerun dindindin ne guda bakwai, daga cikin 26 na kwamiitin sulhu, idan aka fadada shi. Suna kuma neman a bai wa kasashe biyu daga nahiyar masu kujerun dindindin ne, damar hawar kujerar na ki. Sai dai, a ganin Frankfurter Allgemeine Zeitung, za a yi `korafi a kan wadannan bukatun, kamar dai yadda aka yi a kan bukatun da kasashen rukunin G 4 da ya kunshi Jamus, da Indiya, da Brazil da Japan suka gabatar a cikin wannan makon.
A halin yanzu dai, kasashen Sin da Rasha da Amirka, masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun, sun nuna adawarsu ga kudurin da kasashen G-4 din suka gabatar. Sabili da haka ne kuwa, samun goyon bayan kasashen Afirka a wannan yunkurin nasu ke da muhimmanci kwarai. Kuri’unsu a Majalisar dinkin Duniyar zai iya samun gagarumin angizo kan sakamakon amincewa da kudurin, ko kuma yin watsi da shi, inji Frankfurter Allgemeine Zeitung.
Da yake bayyana ra’ayinsa a kan wannan korafin da ake yi, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Kkofi Annan, ya ce bai kamata a daga wannan muhawar da ake yi kan fadada kamitin sulhun ba.