Rahotanni daga Afghanistan sun ce sojan Italiya guda ya mutu, sa’annan wasu biyu suka ji rauni a haɗarin motar da suke ciki. | Labarai | DW | 21.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rahotanni daga Afghanistan sun ce sojan Italiya guda ya mutu, sa’annan wasu biyu suka ji rauni a haɗarin motar da suke ciki.

Ƙungiyar ƙawance ta NATO, ta tabbatad da rahotannin cewa, sojan Italiya guda ne ya mutu, sa’annan wasu biyu kuma suka ji rauni, yayin da motar da suke ciki ta kife, a wani haɗarin da ya auku kusa babban birnin ƙasar, wato Kabul. Rahotanni sun ce sojojin na aikin sintiri ne jiya da yamma, yayin da haɗarin ya auku. A halin yanzu dai, ana jiyyar sojojin da suka jikatan ne a wanni asibitin rundunar NATOn da ke birnin Kabul.