Rahotan shekara-shekara na Amnesty. | Siyasa | DW | 28.05.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rahotan shekara-shekara na Amnesty.

Al'ummomin Duniya na cigaba da rayuwa cikin ƙangi

default

Ƙungiyar kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International ta fitar da rahotanta na shekara-shekara wanda ke bayyana halin ƙunci na talauci da duniya ke ciki da ƙaruwar take hakkokin jama'a a sassa daban-daban na duniya.

Matsalar tattalin arziki da Duniya ke ciki, yana barazana wa rayukan mutane kimanin miliyan 90 waɗanda ke fama da matsanancin talauci. Jagorar ƙungiyar kare hakkin jama'ar ta kasa da kasa Irene Khan tace "muna rayuwa a al'ummar da rashin adalci, tsaro da nuna banbanci yayiwa katutu,wanda kowane lokaci daga yanzu zai iya tarwatsewa".

Kazalika rahotan Amnestin na wannan shekara da aka gabatar a ofisoshin hukamr dake birnen London da Berlin, bayan matsalar tattali ya kuma taɓo yaki da ayyukan tarzoma.

Majalisar Ɗunkin Duniya ta kiyasta cewar Kimanin mutane biliyan 4, wanda ke wakiltan kusan kashi biyu daga cikin uku na yawan al'umma ne, suke rayuwa a inda ake fama da rashin doka da oda. Kasancewar talakawa sune ke fuskantar barazanar take musu 'yanci, kamar yadda Direktan Amnesti International dake wakiltan ƙasashen Turai a birnin Brussels Nicolas Beger yayi nuni dashi..

Symbolbild Marokko NGOs Amnesty International

Amnesty reshen Morokko

"A ra'ayinmu ya zamanto wajibi a yaki talauci ,idan har zaa darajawa talakawa,tare da tabbatar musu da kare 'yancinsu"

A shekarar data gabata dai Amnesty tayi nazarin halin da ake ciki na 'yancin alumma a ƙasashe kimanin 157.

Binciken ya gano cewar a 81 daga cikin wannan adadi ana keta dokar faɗin albarkacin baki. A ƙasashe 50 kuwa mutane da dama sun kasance a tsare sakamakon rigingimu na siyasa da addinai ko kuma kabilanci. Ayayinda a wasu kasashe 27, mutane ke fuskantar azabtarwa a ƙasashensu na asali, ko kuma yanke musu hukuncin kisa.

Wannan batu ya samu suka da kakkausar murya daga Direkatan Turai Nicholas Begers.

Yace: "A ƙasashe 19 dake Turai yadda ake kula da 'yan gudun hijira da masu neman mafaka na siyasa ya saɓawa dokokin kare hakkin jama'a. Ayayinda a wasu ƙasashe 12 ana take 'yancin mutane, da sunan yaki da ayyukan ta'addanci"

Rahotan Amnestin mai shafuna 400, ya yi nazari dangane yadda ake cigaba da take hakkoin jama'a a sassa na Duniya waɗanda suka haɗar da fitattun wurare kamar Darfur ɗin Sudan, Myanmar da yankunan Palastinawa.

A nahiyarmu ta Afirka, ƙungiyar ta soki rigingimu na siyasa da gwamnati kan dauki nauyi a kasashe kamar Zimbabwe, janhuriyar demokaradiyyar kongo, inda akan jefa al'umma cikin halin kaka-ni-ka-yi.

Amnesty International Demonstration für Freilassung von Aung San Suu Kyi

Masu gangamin bukatar sakin Suu Kyi a Myanmar

b

Zaɓen Barack Obama a matsayin shugaban Amurka ya janyo fatan rufe kurkukun gwale gwale na Guantanamou ,sai dai Amnesty tace watanni kalilan bayan watanni kalila, akwai saɓani cikin ayyukan sabuwar karagar mulkin

A nahiyar turai kuwa, Amnsety ta soki yadda tsiraru suka fuskanci wariya sakamakon yaƙin daya gudana tsakanin Rasha da Georgia. In Romawa, yahudawa da Musulmi suka fuskanci ƙiyayya da ƙyama a ɓangaren mutane ko kuma ƙungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi.

Amnestin ta kuma danganta rikicin daya ɓarke a tsakanin Izraela da palastinawa ziringaza a watan janairu, da sakacin ƙin darajawa dokokin ƙasa da ƙasa a ɓangaren sojin yankin. Ƙungiyar dai ta yi nuni dacewar, duniya na fuskantar barazanr karancin abinci, rashin aikin daura da take hakkokin jama'a. Ta tunatar da cewar a yayinda ake kokarin shawo kan matsalar tattalin arziki, ya zamanto wajibi a darajawa hakkokin al'umma.

Mawallafiya: Zainab Mohammed

Edita: Mohammed Nasir Awal