Rahotan mdd kan dumamar yanayi | Labarai | DW | 04.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rahotan mdd kan dumamar yanayi

Sama da kwararru ta fannin kimiyya da fitattun masana kann sauyin yanayi 100 ne,suka amince da matakan da rahotan mdd ta gabatar adanage da yadda zaa kalubalanci matsalolin karuwar dumamamr yanayi.Wannan yazo ne bayan daukan kwanaki 5 ana mahawara a taron swauyin yanayi da mdd ta dauki nauyin gudanjarwa a birnin Bangkok,dake zama fadar gwamnatin Thailand.Rahon mdd na nuni dacewa akwai isassun kayayyakin aiki da fasaha da zaayi amfani dasu wajen yakar matsalar dumamam4r yanayi.Bugu da kari rahotan ya kuma jaddada bukatar shawo kann matsalar fitar da iska mai guba a bangaren masana’antu.