1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Raguwar kudaden taimakon raya kasashe masu tasowa.

Mohammad Nasiru AwalJanuary 26, 2004
https://p.dw.com/p/BvmK
Tun daga shekarar 1990, kudaden taimakon raya kasa da Jamus ke warewa ya ragu da kimanin kashi daya cikin uku. A halin da ake ciki kasafin ya yi kwatankwacin kashi 0.27 cikin 100 na jumlar kudin da kasar ke samu a shekara. Ko da yake daukacin taimakon da Jamus din ke ba kasashe masu tasowa na samuwa ne daga bashin da take yafewa wadannan kasashe, amma kungiyoyin ba da agaji na ganin bai dace hakan ya sa gwamnati ta soke wani kaso na taimakon raya kasa da take ba kasashe masu tasowa ba. An jiyo shugaban kungyiar Germanwatch Ludger Reuke na nuna fargabar cewa muddin aka ci-gaba da rage yawan kudaden taimakon raya kasa, to za´a wayi gari wata rana Jamus ba ta da sauran ayyukan raya kasa da take gudanarwa a ketare.
To sai dai a wannan lokaci da gwamnati ke daukar matakan tsuke bakin aljihu kana kuma take soke tallafin da take ba jama´a a bangarori da dama na rayuwa, zai yi wuya gwamnatin tarayya ta iya yiwa jama´ar kasar nan bayanan dalilan da zasu sanya ta kara yawan kudaden da take warewa ayyukan taimakon raya kasa a ketare.
To amma duk da haka kungiyoyin da ba na hukuma ba na kira ga gwamnati da kada ta dakushe ayyukan ma´aikatar ba da taimakon raya kasa ta amfani da manufofin wasu hukumomi daban. Alal misali shirin bunkasa kasuwannin kasashe masu tasowa, wanda bai yi nasara ba, saboda kudaden tallafi da kungiyar tarayyar Turai ke ba manomanta, musamman game da kayan amfanin gona da suke fitarwa zuwa ketare.
Kamata yayi gwamnati ta kara yawan taimakon da take ba kasashe masu tasowa musamman dangane da ayyukan raya kasa, idan ba haka ba kuwa to matsalolin wadannan kasashen zasu kara ta´azzara ne, inji Ludger Reuke na kungiyar Germanwatch. Mista Reuke ya kara da cewa ko da yake dole ne Jamus ta magance matsalolin iri daban-daban da take fuskanta, amma bai kamata ta juyawa kasashe masu tasowa baya ba.
Dole ta cika alkawuran da take yi na ba da taimakon raya kasa.
Wani babban hadari da kungiyoyin da ba na gwamnati suke gani shine idan a nan gaba aka hada aikin wanzar da zaman lafiya a ketare da kudaden da ake warewa ayyukan taimakon raya kasa. Domin bisa ga dukkan alamu hukuma na shirin hade ayyukan taimakon raya kasa da wasu ayyuka kamar na tura dakarun kiyaye zaman lafiya a kasashe masu tasowa. Muddin aka yi haka kuwa to ke nan ba za´a iya ci-gaba da aiwatar da babbar manufar aikin raya kasa kamar samar da ruwan sha, kiwon lafiya, ba da ilimi da dai sauran su ba.