1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rage 'yunwa a duniya

September 19, 2010

Jamus ta yi ƙira ga shugabannin duniya da su ƙara hoɓɓasa wajen rage 'yunwa da talauci a duniya.

https://p.dw.com/p/PFuM
Angela MerkelHoto: AP

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi ƙira ga shugabannin duniya da su ƙara ɗaukan matakai na kawar da 'yunwa da talauci. A jawabin mako-mako da ta ke yi, Merkel tace kekkewan labarine rohoton da aka samu na cewa an samu raguwar waɗanda ke fama da 'yunwa da kimanin mutane miliyan ɗari a bara. Tace amma yaƙi da talauci yana tafiyar hawainiya. Merkel ta yi jawabin ne kafin a yau ta tashi zuwa birnin New York don hallartar taron MƊD da zai tattauna batun rage talauci a duniya cikin tsarin muradin ƙarni wato MDGs. Ana saran halartan fiye da shugabannin ƙashen duniya ɗari a taron na New York. Biyu daga ƙudurorin muradun ƙarni na MDGs shine a rage 'yunwa da talauci da kusan rabi nan da shekaru biyar masu zuwa.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu