1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rage sojin Amurka a Iraqi

Fadar Gwamnatin Amurka ta tabbatar da cewa babban kwamandan sojin Amurkan a Iraqi janar George Casey ya tsara shirin rage yawan sojin Amurkan a kasar Iraqi. Sai dai shugaban Amurkan George W Bush ya nanata cewa duk wani shirin janye sojojin zai dogara ne ga kwazon sabbin dakarun Iraqin na iya kula da shaánin tsaron kasar. An ci gaba da fuskantar tashe tashen hankula a Iraqin bayan harin bom a wasu kasuwanni biyu a Hilla da Baqouba da ya hallaka mutane da dama kwana daya bayan da P/M Iraqin Nuri al Maliki ya gabatar da shirin sasantawa da hadin kan kasa.