Rage hayaƙin masana′antu a Jamus | Labarai | DW | 05.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rage hayaƙin masana'antu a Jamus

Majalisar ministoci ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta amince da shirin rage hayaƙin masana´antun Jamus da kudinsa ya kama miliyoyin euro.

Wannan shiri na bukatar rage hayaƙin masana’antu da kashi 36 daga cikin ari.Wannan mataki ne, da zai rage hayaƙin masana’antu da ton miliyan 220.Zai kuma buƙaci karin yin anfani da makamashi yanda ya kamata.Wannan shiri matakin farko ne na wani shiri da aka zayyana a watan Agusta da ya shige, da ya hada da rage hayaƙin motoci.