1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rafsanjani ya samu nasara a Zaben majalisar kwararru

Maaikatar harkokin cikin gida ta kasar Iran ta tabbatar da gaggarumar nasara da tsohon shugaba Hashemi Rafsanjani ya samu a zaben majalisa da aka gudanar.

Sakamakon karshe na na zaben na ranar jumaa,ya nuna cewa Rafsanjani ya samu kuriu ribi biyu fiye da dan takara da jamiyar masu tsatsauran raayi ta Ahmedinajad ta tsayar.

Ana kuma sa ran jamiyar Rafsanjani mai sassaucin raayi da jamiyar masu neman sauyi zasu samu kujeru da dama cikin zaben majalisar birnin Tehran.

A gobe talata ake sa ran samun sakamakon karshe na zaben kananan hukumomi.

Duk da cewa zaben na ranar jumaa ba zaiyi tasiri ga manufofin wajen kasar ba,amma kasasahen yammacin duniya zasu yi maraba da alamun dake nuna cewa farin jinin Ahmedinajad na raguwa.