1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rabuwar kanu cikin jam´iyar adawa ta UFC a Togo

May 29, 2010

Jam´iyar UFC mai adawa a Togo ta tsige shugabanta Gilchrist Olympio don ya amince da girka gwamnatin haɗin kan ƙasa

https://p.dw.com/p/NclO
Jean-Pierre Fabre ya ba da sanarwar tsige Gilchrist Olympio daga UFCHoto: AP

A birnin Lome na ƙasar Togo dubun dubatar jama´a ne, suka shirya zanga-zangar lumana, domin nuna goyan baya ga matakin da shugaba Faure Yasimbe ya ɗauka na girka gwamnatin haɗin kan ƙasa, wadda ta ƙunshi babbar jam´iyar adawa ta UFC.

Dalili da girka wannan gwamnati an samu rabuwar kanu a jam´iyar ta UFC.Wani gungun membobi a komitin ƙoli ya yanke shawarar tsige shugaban jam´iyar Gilchrist Olympio wanda ya rattabawa yarjejeniyar hannu ranar Laraba da ta wuce.

Jean Pierre Fabre ɗan takara jam´iyar UFC a zaɓen shugaban ƙasar Togo da ya wakana a watan Maris na wannan shekara ya ce Gilchrist Olympio, ya yanke wannan shawara ba tare da sanin uwar jam´iya ba.

Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Mohamed Nasiru Awal