1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girika a ƙungiyar EU

Karamanolis, Alkyone May 13, 2008

´Yan Girika suna jin daɗin kasancewar ƙasar cikin tarayyar Turai

https://p.dw.com/p/DzAZ
Firaministan Girika Costas Karamanlis da matarsa NatassaHoto: AP

Jama´a masu sauraro barkanku da warhaka, barkanmu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Mu Kewaya Turai, shirin da ke kawo muku batutuwan da suka shafi siyasa, tattalin arziki, al´adu, zamantakewa da kuma dangantaka tsakanin kasashen nahiyar Turai.

A bana a nahiyar Turai za mu yi hutu ko ya kamata ´ya´yanmu su nemi ƙarin ilimi a Turaui. Waɗannan dai su ne furuce furucen da a kullum ake ji a ƙasar Girika. A haƙiƙa tun a shekara ta 1981 ƙasar ta Girika ke cikin ƙungiyar tarayyar Turai EU, to amma gabanin shigar da ƙasar Bulgariya cikin ƙungiyar ta EU a cikin shekarar da ta gabata, Girika ba ta da iyaka ta bai ɗaya da wata ƙasa ta ƙungiyar EU. Duk da haka dai ´yan ƙasar sun daɗe suna jin daɗin kasancewarsu cikin ƙungiyar EU duk da wasu shakkun da ba a rasa ba. To shirin na yau zai leƙa ƙasar ta Girika ne don jin ra´ayoyin al´umar ƙasar a dangane da ƙungiyar EU da kuma tasirin ƙungiyar a cikin ƙasar.

A unguwar manyan kantuna dake Athens babban birnin Girika ana samun duk abin da ake bukata kama daga aku zuwa injin nome haki, makullayya da labule. A cikin yanayin zafi na sommer da lokacin sanyin hunturu, ƙofofin kantuna na kasancewa a buɗe don ka da a yi asarar abokanen hulɗar kasuwanci sannan a ɗaya hannun kuma don ci-gaba da hulɗa da maƙwabta. Wani mai shago a yankin da ake kira Panayotis Stavropoulos ya na sayar da abubuwa da dama a kantinsa ciki har da hotunan shararrun mutane a duniya, turaren wuta da dai sauransu. Stavropoulos mai shekarun haihuwa tsakanin 40 zuwa 50 har yanzu yana tune da matsayin ƙasar Girika gabanin a ɗauke ta cikin ƙungiyar tarayyar Turai a shekara ta 1981.

Stavropoulos:

“An samu canje canje masu tarin yawa Girika a cikin shekaru 25 da suka gabata. Maƙudan kuɗaɗe sun shigo ƙasar, sannan an samar da abubuwan more rayuwa kamar hanyoyin sadarwa na zamani. Bugu da ƙari mun samu ci-gaban fasaha a rayuwarmu ta yau da kullum. Waɗannan dukka abubuwa ne na ci-gaba a fannoni daban daban. To amma muna da matsaloli, kamar yawan marasa aikin yi, rashin tabbas na ɗorewar wuri aiki sai kuma ƙarancin albashi. Waɗannan abubuwa ne da ke da alaƙa kai tsaye da tarayyar Turai, domin a birnin Brussels a tsayar da dukkan shawarwari masu muhimmanci. Amma duk da haka ina iya cewa an samu ci-gaba a wasu ɓangarorin, yayin da aka samu akasin haka a wasu ɓangarori.”

Ita kuwa mahaifiyar Panayotis Stavropoulus, wadda ita ma ta ke zamna a kantin tana mai ra´ayin cewa ƙirƙiro da takardun kuɗi na Euro ya kawo canje canje da dama.

Misis Stavropoulus:

“Abubuwa da dama sun canza sakamakon ɓullo da takardun kuɗi na Euro. Duk komai ya yi tsada kama daga abinci ya zuwa tufafi da dai duk kayan masarufi. Da wuya albashinka na wata ke isan ka. Hakazalika cinikin da muke yi a wannan kanti ya ragu, domin mutane ba su da kuɗin kashewa.”

Ɗaya daga cikin masu kantuna da har yanzu yake ciniki shi ne Mista Giorgos mai sayar da riɗi. Abokan cinikinsa sun sa shi ƙwarai da gaske. A duk lokacin da suke kan hanyar zuwa aiki su kan tsaya kantinsa su saye riɗi kana kuma su ɗan zanta da shi kafin su ƙarasa wurin aiki. Mista Giorgos ya kan samu lokacin yin hira ko tuna baya. A dangane da batun na nahiyar Turai Giorgos na mai ra´ayin cewa.

Giorgos:

“Ƙungiyar tarayyar Turai EU ta canza suffar siyasar duniya. Da farko dauloli biyu wato Amirka da Rasha kaɗai suka yi ta juya akalar siyasar duniya. Amma yanzu mu ne a sahu na uku. Ban da haka ga takardun kuɗi na Euro wanda ke taka muhimmiyar rawa a harkokin siyasa da tattalin arziki na duniya. Mu ma ´yan Girika yanzu muna jin ƙafarmu ta kama ƙasa sosai. Domin a matsayin mu na ´yan ƙungiyar EU, mun fita daga jerin ƙasashen da manyan daulolin duniya ke wasa da hankalinsu. Haɗaɗɗiyar nahiyar Turai wata aba ce ta daban.”

Shi ma Loukas Tsoukalis na cibiyar nazarin manufofin siyasa ta Eliamep ya tabbatar da haka. Ya ce har yanzu wasu ´yan Girika musamman masu ra´ayin kishin kasa da masu sukar shirin haɗakar duniya suna nuna shakku ga kungiyar EU. Suna danganta manufofin EU musamman dangane da yanke shawarwari da ´yan ra´ayin sakarwa harkokin kasuwanci mara ba tare da la´akari da tasirinsa cikin wata ƙasa ba. To amma duk da haka Girika kasa ce mai ƙaunar manufofin ƙungiyar EU. Ƙuri´ar jin ra´ayin jama´a ta yi nuni da cewa kimanin kashi 60 zuwa 70 na ´yan ƙasar ta Girika suna goyon bayan kasancewar ƙasar su a cikin tarayyar Turai.

Tsoukalis:

“Shigar da ƙasar ta Girika cikin ƙungiyar EU ya ɗaga darajarta daga wata ´yar diplomasiya ta EU zuwa wata ƙasa da ake damawa kuma sha da ita a cikin EU. Hakazalika ɗaukarta cikin ƙungiyar ta EU tamkar an warware mata wata matsala ce da ta daɗe tana ci mata tuwo a ƙwarya. Domin har yanzu akwai masu ƙyamar Amirka a cikin ƙasar domin da yawa daga cikin ´yan Girika na masu ra´ayin cewa Amirka ce ta marawa gwamnatin mulkin sojin ƙasar daga shekarar 1967 zuwa 1974. Saboda haka shigar da ita cikin EU ya ba ta damar kasancewa cikin ƙasashen yamma ba tare da ta dogara ga ƙasar Amirka ba.”

Panagiotis Stavropoulos wanda a kantinsa ya ke auna ma wani abokin cinikinsa turaren wuta, ya ce a wani ɓangaren kasancewarsu a cikin ƙungiyar EU na da fa´ida duk da sukar da wasu ´yan ƙasar ke yi.

Stavropoulos:

“Gaskiya ba na jin daɗi idan ƙungiyar EU ta tsoma bakinta a cikin harkokin cikin gidan Girika. To amma a hankalce daidai ne idan hedkwatar EU dake birnin Brussels ta kula da yawan kuɗaɗen da take turo mana cikin wannan ƙasa, musamman a fannin kare kewayen ɗan Adam."