1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ra'ayoyin wasu daga cikin jaridun Jamus a kan nahiyar Afirka.

YAHAYA AHMEDOctober 27, 2006

A cikin sharhohin da suka buga kan nahiyar Afirka a wannan makon, jaridun Jamus sun fi mai da hankalinsu ne kan yankin Afirka ta Yamma, inda suke ganin rikice-rikice da ke ta kunno kai kamar a Najeriya ko a Côte d’Ivoire, za su iya janyo taɓarɓarewar al’amura da wahalhalu da yawa ga al’umman wannan yankin, idan ba a ɗau sahihan matakai wajen magance matsalar ba.

https://p.dw.com/p/BvPZ
Wasu daga cikin jaridun da ke fitowa a ko wace rana a Jamus.
Wasu daga cikin jaridun da ke fitowa a ko wace rana a Jamus.Hoto: AP

Da farko dai jaridar Der Tagesspiegel ta dubi halin da ake ciki ne yanzu a tarayyar Najeriya, inda watanni 6 kafin a gudanad da zaɓe, ake ta samun taɓargaza iri-iri na cin hanci da rashawa, abin da take gani zai iya janyo taɓarbarewar al’amura a huskar siyasar ƙasar da ma na yankin Afirka Ta Yamman gaba ɗaya.

Ƙololuwar wannan taɓargazar dai inji jaridar, ita ce tsige gwamnan jihar Ekiti da aka yi. Ta ce ana zarginsa ne da juya kuɗin jama’a zuwa ajiyar bankinsa da kuma karɓar cin hanci da rashawa. Der Tagesspiegel ta ƙara da cewa, halin da ake ciki a Ekitin ne ya sanya shugaba Olusegun Obasanjo kafa dokar ta ɓaci a jihar da kuma naɗa wani tsohon babban hafsa na rundunar sojin ƙasar tamkar kantoman jihar. Shi dai Obasanjo na hujjnata matakin da ya ɗauka ne da cewa, da akwai barazanar shiga wani hali na mulkin ruɗu a jihar. Amma masu sukar wannan lamirin na zargin Obasanjon da muƙarrabansa ne da yin amfani da matakan yaƙi da cin hanci da rashawa wajen fatattakar abokan hamayyarsu kafin a gudanad da zaɓen shugaban ƙasar a cikin watan Ifirilu mai zuwa. Wasu kuma na sukar Obasanjon ne da janyo tashe-tashen hankullan da gangan, don ya tsawaita wa’adinsa.

Rigingimun siyasa da ake ta yi a ƙasar na barazanar janyo wargajewar tsarin tarayya da Najeriyan ke bi, inji Der Tagesspiegel. A halin da ake ciki dai Obasanjo ba zai iya tsayawa takaran zaɓe a wa’adi na 3 ba, tun da majalisar dattijan ƙasar ta ƙi amincewa da shirinsa na ta zarce. Amma mataimakinsa Atiku Abubakar ma, ana zarginsa da cin hanci da rashawa. Babu kuma kyakyawar hulɗa tsakanin shugaba Obasanjon dav mataimakin nasa, waɗanda a halin yanzu ma, bas a ga maciji da juna. Rikice-rikicen da ake yi a yankin Naija-Delta mai arzikin man fetur kuma na ƙara janyo hauhawar tsamari a ƙasar.

Jaridar Neues Deutschland , ita ma ta yi sharhi ne kan yankin na yammacin Afirka, inda ta yi nazari game da ziyarar da shugaban ƙasar Benin, Boni Yayi, ya kawo a nan Jamus.

Benin dai, inji jaridar, tana ɗaya daga cikin ƙasashe 20 mafi talauci a duniya. Sabili da haka, ƙasar na dogaro ne kan samun taimako daga ƙasashen ƙetare. Amma duk da talaucinta, ta kasance ƙasa mai bin tafarkin dimukraɗiyya, wadda kuma a mizanin auna salon tafiyad da kyakyawar mulki a nahiyar Afirka, take ɗaya daga cikin waɗanda za a iya ba da misalai da su. Shi dai shugaba Boni Yayi, inji Neues Deutschland , ya sanya manufar ƙarfafa tafarkin dimukraɗiyya da kuma inganta tattalin arzikin ƙasar ne tamkar muhimman jigoginsa, inda yake ba da fiffiko ga fafutukar yaƙi da talauci. A cikin wata fira da ya yi da maneman labarai a lokacin ziyarar tasa a birnin Berlin, shugaba Boni Yayi, ya bayyana cewa nauyin da ya rataya a wuyar shugabannin Afirka ne su tabbatad da ganin cewa sun tafiyad kyakyawan mulki, kuma sun inganta tsarin rarraba madafan iko don nuna adalci ga duk al’umma. Su ko ƙasashe masu ci gaban masana’antu da mawadata kamata ya yi su aiwatad da alkawarin da suke ta ɗauka na yafe wa ƙasashen Afirkan basussukansu.

Ita ko jaridar Neue Zürcher Zeitung, ta yi sharhi ne kan halin da ake ciki a ƙasar Côte d’Ivoire. Duk da tsawaita wa’adin shugaba Laurent Gbagbo da shekara ɗaya, da kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi, har ila yau dai ba a samo bakin zaren warware rikicin wannan ƙasa ba tukuna. A halin yanzu dai, kira kawai jami’an kwamitin sulhun suka yi, ga duk ɓangarorin da ke rikici da juna a Côte d’Ivoire ɗin da su koma kan teburin shawarwari don su cim ma daidaito kan tsara wa ƙasar sabuwar alƙibla. Jaridar ta ari bakin babban jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da shirya zaɓe a ƙasar, Gérard Stoudmann, yana mai cewar, dole ne a cim ma madafa a ƙasar a shekara ta 2007, idan ana son kau da barkewar wani mummunan rikici da kuma ƙara taɓarrbarewar al’amura a Côte d’Ivoiren. Jama’a da dama ne dai a ƙasar ke nuna ɓacin ransu ga yanayin cijewar al’amura da ake ta fama da shi a halin yanzu.

Kawo yanzu dai, inji Neue Zürcher Zeitung, babu wani ɓangaren da ya fito ya bayyana shirinsa na taimakawa wajen neman hanyoyin sulhunta rikicin. Har ila yau kuma, ba a sami wani ci gaba ba, a yunƙurin kwance wa masu yaƙan juna a ƙasar ɗamara da kuma gano ainihin ’yan ƙasar, waɗanda suka cancanci a yi musu rajista don su iya ka da ƙuri’u a zaɓen shugaban ƙasar. A ganin jaridar dai, kafin a iya gudanad da zaɓe cikin lumana da kwanciyar hankali a Côte d’Ivoiren, sai an inganta halin tsaro a ƙasar.

Jaridar Die Zeit kuma, ta mai da hankalinta ne kan yankin Darfur na ƙasar Sudan, inda ta yi kakkausar suka ga yadda ƙasashen Turai ke zaman oho ba ruwanmu suke kallon yadda ake ta yi wa al’umman yankin masu baƙaƙen fata abin ta kira kisan kiyashi. Tambayar da ta yi ita ce, an ƙi ɗaukan mataki don kare al’umman yankin ne daga wannan annobar saboda su baƙaƙe ne, ko kuwa? Kawo yanzu dai, inji jaridar, rikicin yankin ya janyo asarar rayukan mutane fiye da dubu ɗari 2, sa’annan kusan mutane miliyan 3 ne rikicin ya mai da su ’yan gudun hijira. Ana nan kuma ana ta ci gaba da yi wa baƙen fatan yankin kisan kiyashi, inda ’yan ƙungiyar Larabawan na ta Janjaweed mai samun ɗaurin gindin gwamnatin birnin Khartoum ke ta cin karensu babu babbaka. Za a iya cewa dai ana huskantar barazanar ɓarkewar wata annoba kamar irin ta Ruwanda, inji Die Zeit . Sai dai a wannan karon, ƙasashen Yamma ba su da wani uzuri na cewa ba su san abin da ke aukuwa a Darfur ɗin ba ne, kamar dai yadda suka yi game da batun Ruwanda a shekarar 1994. Shekaru 12 bayan kisan kiyashin Ruwanda dai, bai kamata a ce an sa ido ana ganin sake aukuwar wannan ɗanyen aikin ba. Nauyin hana aukuwar wata sabuwar annobar kuwa ya rataya ne a wannan karon a wuyar ƙasashen Yamma. Za su iya ɗaukan matakan kawo ƙarshen wannan ɗanyen aikin, saboda suna da hanyoyin yin haka. Idan ko ba su yi ba, to saboda dalili daya ne kawai. Wato saboda masu baƙaƙen fata ne kawai ke mutuwa. Me kuwa ya yi musu zafi? Jaridar ta Die Zeit , ta kammala sharhinta ne da cewa, idan hakan kuwa ya auku, to tarihi ba zai taɓa yafe musu ba.