1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ra’ayoyin masu sauraro sashen Hausa

Thomas MöschOctober 31, 2013

"DW ta kasance abin alfahari a gare ni, ta kasance alƙibla ta ga dukkan al'amura na yau da kullum" - Umaru Ginsau, Nijar.

https://p.dw.com/p/1A9aj

Ni mutum ne mai sha'awar sanin abubuwan da ke faruwa a ƙasashen duniya sosai, tun daga wancan lokaci har a yau. Saboda wannan dalili da kuma wasu masu yawa na fara sauraren sashen Hausa na DW. Hakika ina yin alfahari da ku a sashen Hausa don na ƙaru sosai a sanadin sauraren nagartattun shirye-shiryenku.
Alhaji Yahaya Salihu Makaniken Mota

A zahirin gaskiya babu wanda gidan rediyon DW sashen Hausa ya canza wa rayuwa kamar ni, saboda shirye-shiryen da kuke gabatarwa masu ilmantarwa, faɗakarwa da nishaɗantarwa. Misali ‘Ra'ayin Matasa', 'Lafiya Jari', ‘Mutum da Duniyarsa' da sauransu.
Adamu Aliyu Amo, Katsina, Najeriya


Ina taya ku murnar cika shekaru 50 da kuka yi. Bayan haka wannan gidan rediyo naku muna jin daɗin shirye-shiryenku wanda kuke yi musamman ma shirinku na ‘Ji Ka ƙaru' da ‘Wasiƙun masu Sauraro' da sauransu. Ina fatan za'a maido da shirin koyon harshen Jamus domin gaskiya muna jin daɗin wannan shiri.
Aminu Abdu Hashim Zangon Daura

Quelle: Isidore Doudou. Verantwortlich für das Hörer Klub von ABIDJAN - Elfenbeinküste Les amis de la Deutsche Welle Wo ? ABidjan was ? das Hörer Klub von der DW in Abidjan => Aktionen in Schule, um über die DW zu sprechen
Hoto: Les amis de la Deutsche Welle

Shekaru da yawa baya, lokacin ina ƙarami mahaifina ya kasance mai sauraron wannan gidan rediyo na DW a kowane lokacin da suke gabatar da shirye-shiryensu. Ni kuma a yarintata ina son rediyo ina kuma ƙaunar zama kusa da rediyo ta. Da haka ne na tashi da sauraron wannan gidan rediyo a raina, ya kasance ko da mahaifina ba ya nan in lokaci ya yi sai na zo na buɗe rediyon na kama Jamus. Da haka har na girma yadda zan iya mallakar rediyo tawa ta kaina, kuma saboda Jamus na mallaki rediyo, wanda a yanzu haka na zama saurayi ɗan shekaru ashirin da biyar.
Abdullahi Musa Babaru, Hadeja, Najeriya

Babban dalilin da ya sa alaƙa ta da Rediyo Jamus ta ci gaba da kasancewa shi ne, irin matsayin taka-tsantsan da gidan rediyo yake bi ga al'amuran siyasar duniya. Ko da yake ƙasar Jamus ba ta shisshigi a cikin al'amuran siyasar ƙasashe, amma yadda gidan rediyo yake ƙin nuna goyon bayansa ga wani ɓangare in an samu rikicin siyasa a wata ƙasa, shi ne babban dalilina na ci gaba da alaƙa da wannan gidan rediyo.
Uba Yaro Mohammed, Gashua, Jihar Yobe, Najeriya


A gaskiya ban taɓa sanin 'yancina ba sai da na fara sauraron wannan tasha ta DW, musamman ma yadda suke ba ni dama ba dare ba rana wurin faɗar ra'ayina. Gaskiya ni kam na ɗauki wannan tasha tamkar makarantar jami'a don ya wayar da ni ta hanyoyi da dama.
Abdulwahab Haladu Zarma Hina

Quelle: Isidore Doudou. Verantwortlich für das Hörer Klub von ABIDJAN - Elfenbeinküste Les amis de la Deutsche Welle Wo ? ABidjan was ? das Hörer Klub von der DW in Abidjan => Aktionen in Schule, um über die DW zu sprechen
Hoto: Les amis de la Deutsche Welle

DW ta kasance abin alfahari a gare ni, ta kasance alƙibla ta ga dukkan al'amura na yau da kullum.
Umaru Ginsau, Duci, Nijar

Dangantakata da rediyo DW alheri ce da jin daɗi gare ni, domin ta ilimintar da ni sanin rayuwa da tafiya ta zaman duniya. Godiya ga DW domin yaɗa labarai na gaskiya da adalci.
Oumarou Tallou, Zinder, Nijar

Na fara sauraren wannan gidan rediyo na DW bayan buɗe shi da shekaru huɗu, wato a shekara ta 1957. Ga shi na aiko muku da mujallar nan ta Turanci wato "Hallo Friends", wadda aka aiko mini a wancan lokacin.
Alhaji Umaru Babanyara, Bichi, Jihar Kano, Najeriya