1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ra'ayoyin jaridun Jamus kan nahiyar Afirka a wannan makon

YAHAYA AHMEDJune 16, 2006

Duk da gasar ƙwallon ƙafa ta cin kofin duniya da ake yi yanzu a nan Jamus dai, jaridu nan ƙasar da dama sun yi sharhohi kan wasu ababan da ke wakana, kuma suka fi jan hankulla a nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/BvPr

A wannan makon, jaridun Jamus da dama ne suka yi sharhohi kan nahiyar Afirka, abin da ba a zata ba, saboda hayaniyar gasar ƙwallon ƙafa ta cin kofin duniya da ake gudanarwa yanzu a nan ƙasar.

Manyan jaridu kamarsu Frankfurter Allgemeine Zeitung da Neues Deutschland da Tageszeitung, sun takalo batutuwan da a halin yanzu suka fi jan hankulla ne a nahiyar ta Afirka, alal misali kamar batun zaɓe a kasar Jumhuriyar Dimukraɗiyya ta Kwango, ko amincewar da Najeriya ta yi ta janye dakarunta daga tsibirin Bakassi da dai sauransu.

Mummunan halin da ɗimbin yawan baƙin haure daga nahiyar Afirka ke te samun kansu a ciki, a yunƙurin da suke yi na shigowa nahiyar Turai ko ta yaya, na cikin jigogin da jaridar Neues Deutschland ta yi sharhi a kansu tgame da nahiyar ta Afirka a wannan makon.

Duk da tsauraran matakan da hukumar tsaron iyakar bakin teku ta ƙasar Spain ke ɗauka na sace wa baƙin haure daga nahiyar Afirka iska dai, ba ta cim ma nasara ba tukuna, inji jaridar. Saboda su dai baƙin hauren, kamar sun lashi takobi ne na shigowa nahiyar Turan ko a mace ko a raye. Neues Deutschland ta ƙara da cewa, tun farkon wannan shekarar, kusan baƙin haure dubu 11 ne suka sami isa kan tsibirin nan na Canaries, wanda ke ƙarƙashin mulkin ƙasar Spain. Ba a dai taɓa samun yawan wannan adadin ba, sai a wannan shekarar.

Ƙasar Spain, inji jaridar, ta ƙara yawan jami’an tsaron iyakar bakin tekunta, inda suke ta sintiri cikin jiragen ruwa don hango kwale-kwalen da baƙin hauren ke shigowa zuwa tsibiran nata. Amma duk da haka, ba su iya hana dubu 11 daga cikinsu shigowa ba. Wasu alƙaluman da da Hukumar jami’an tsaron iyakar ta Spain ta bayar na nuna cewa, baƙin haure tsakanin dubu da ɗari 2 zuwa dubu da ɗari 7 ne suka rasa rayukansu, a haɗurran kwale-kwalen da ke jigilarsu zuwa tsibirin na Canaries. A galibi dai, inji jaridar Neues Deutschland, mafi yawan baƙin hauren daga ƙasashe daban-daban na yammacin Afirka, suna bi ƙasa ne daga ƙasashensu zuwa Senegal ko Murteniya. Daga nan ne kuma suke samun masu jigilarsu da kwale-kwalen, zuwa tsibiran na Spain. Sai dai, a lokuta da dama, yaudarasu ake yi. Kwale-kwalen da ake amfani da su, ba su dace da safara kan teku ba. Sabili da haka ne kuwa, ake ta munanan haɗurra, waɗanda ke janyo asarar rayuka na mafi yawa daga cikin baƙin hauren.

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, ta yi sharhi ne kan sanarwar da Najeriya ta bayar, ta amincewa da shiga tsakanin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi, wajen sasanta rikicin da take yi da ƙasar Kamaru, kan tsibirin nan na Bakassi, mai arzikin man fetur. Tun fiye da shekaru 10 ke nan dai da Najeriya da Kamaru suka yi ta rikici kan wannan tsibirin, inji jaridar. A cikin shekarun 1990 ma, sai da aka kusa kai ga gwabza yaƙi tsakaninsu.

Jaridar ta ƙara da cewa, bisa yarjejeniyar da aka cim ma a birnin New York a ran litinin da ta wuce, Najeriya za ta janye dakarunta daga tsibirin ne a cikin kwanaki 60 masu zuwa. Bisa yadda al’amura za su kasance dai, Majalisar Ɗinkin Duniya za ta iya tsawaita wannan lokacin da kwana 30. Yarjejeniyar dai ta tanadi bai wa Najeriya har tsawon shekaru biyu, inda za ta miƙa harkokin hukuma na tsibirin ga Kamaru. Su ko mazauna yankin, waɗanda ke matuƙar adawa ga shirin mai da tsibirin ƙarƙashin ikon Kamaru, ita Kamarun a nata ɓangaren, bisa dai ƙa’idodjin yarjejeniyar, za ta ɗau alkawari ne na barinsu a nan, ba tare da korarsu zuwa Najeriya ba. Bugu da ƙari kuma, za a kafa wani kwamiti, wanda zai ƙunshi wakilai daga ƙasashen biyu da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya, don sa ido wajen ganin an aiwatad da ƙa’idojin yarjejeniyar kamar yadda aka tsara.

Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Kofi Annan, inji jaridar, ya bayyana matuƙar farin cikinsa ga amincewar da Najeriya ta yi da yarjejeniyar, kuma ya ce wannan sasanta rikicin iyakar da aka yi, cikin kwanciyar hankali, wato wani abin kwaikwayo ne ga sauran ƙasashe, musamman na nahiyar Afirka. Jaridar ta ari bakin Kofi Annan yana mai cewar, ofishin manzancin Majalisar a ƙasashen Eritrea da Habasha, na kashe kusan dola miliyan ɗari 2 a ko wace shekara, ba tare da ƙasashen biyu sun amince da yarjejeniyar warware rikicin iyakarsu, da aka cim ma a cikin shekara ta 2000 ba. Amma ga shi an cim ma gagarumar nasara a rikicin Najeriya da Kamaru, inda kwamitin sasantawar da aka kafa, dola miliyan 5 kawai yake kashewa a ko wace shekara.

A cikin wani sharhin kuma, jaridar ta Frankfurter Allgemeine Zeitung, ta dubi hidimomin da ake yi ne na shirya zaɓe a ƙasar Jumhuriyar Dimkuraɗiyya Ta Kwango, inda Ƙungiyar Haɗin Kan Turai, wato EU ma, za ta tura dakarunta don kare lafiyar jama’a da kadarori a lokacin wannan zaɓen. Jaridar ta ce, dakarun ƙasa da ƙasa na ƙungiyar EUn za su kasance a Kwangon ne har tsawon watanni 4, wato daga ƙarshen watan Yuli mai zuwa, har zuwa ƙarshen watan Nuwamba. Za a dai gudanad da zagaye na farko na zaɓen ne a ran 30 ga wannan watan. Sa’annan a ran 15 ga watan Oktoba ne kuma za a yi zaɓen shugaban ƙasar, da na jihohi. Ba za a dai ba da sakamakon duk zaɓukan ba kafin ran 30 ga watan Nuwamba.

To jama’a a taƙaice dai, abin da za mu iya kawo muku ke nan game da ra’ayoyin jaridun Jamus a kan nahiyar Afirka a wannan makon.