1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ra'ayoyin jaridun Jamus a kan nahiyar Afirka

YAHAYA AHMEDNovember 11, 2005

A wannan makon, kusan duk jaridun Jamus sun kara mai da hankalinsu a kan nahiyar Afirka. Wannan kuwa ba abin mamaki ba ne, saboda a karshen makon da ya gabata ne, shugaban Tarayyar Jamus Horst Köhler, ya yi wani taron koli da shugabannin kasashen Afirka guda 3, karkashin shirin nan da ya kirkiro na tuntubar juna tsakanin Jamus da nahiyar Afirka. Taron, wanda shi ne na farko irinsa ya sami halartar shugabannin Najeriya da na Afirka Ta Kudu da kuma Habasha.

https://p.dw.com/p/BvQF

Mafi yawan jaridun sun yi sharhi ne kann muhimmancin taron da kuma dalilin yinsa. Akwai dai ra’ayoyi daban-daban da jaridun suka bayyanar a sharhohinsu, wasu na yabo ga shugaba Köhler da shirya taron, wasu kuma na suka da rashin ganin sakamakon da aka samu.

Game da abin da aka cim am a taron ne jaridar General-Anzeiger ta yi sharhinta, inda ta ce:-

"Shawarar da shugaban kasa Horst Köhler ya dauka ta shirya wannan taron don tattaunawa da `yan siyasar Afirka masu neman sauyi da ci gaba, da kwararrun masana a fannoni daban-daban da masu sukar lamiri, da kungiyoyin sa kai na fararen hula da maneman labarai, wani gagarumin mataki ne na samo bakin zaren warware wasu matsalolin da nahiyar Afirkan ke huskanta. Taron dai ya gudana ne cikin lumana, ba tare da jin nauyin tilas ne a cim ma sakamako ba. Rashin ba da wani sakamako ko ta yaya din kuwa, shi ne abin da ya sa kafofin yada labarai da yawa suka yi ta sukar shirin ma gaba daya. Amma ai ba taro ne na gaggawa ba, ko na yin dogon turanci da ba da bayanai iri-iri, wanda a karshe, babu wani sahihin abin da ya haifar. Wannan taro ne na tutunbar juna, na tabbatad da samun fahimtar juna tsakanin masu fada a ji a nahiyar Turai da kuma ta Afirka. Idan an cim ma wannan fahimtar aka kuma sami yanayi na yarda da juna, to daga nan ne za a fara daukan matakan shawo kan matsaloli daban-daban da ake ta fama da su, kamarsu talauci da gurbacewar yanayi, da kaura da dai sauransu. Babu shakka, ba za a iya faranta wa kowa rai, wajen shirya taro irin wannan ba. A lal misali da akwai alamar tambaya a kan gayyatar Firamiyan Habasha Meles Zenawi da aka yi, tamkar daya daga cikin wadanda za su jagoranci Afirka wajen kyautata makomarta.

Amma abin da ke da muhimmanci a nan shi ne, za a ci gaba da irin wannan tuntubar, da shugaba Köhler ya kirkiro.“

Jaridar General-Anzeiger ke nan.

A daidai lokacin da ake taron koli na birnin Bonn, tsakanin shugaba Köhler da shugabannin Afirka ne kuma, a kasar Habasha, wani rikici ya barke inda magoya bayan jam’iyyun adawar kasar suka yi ta zanga-zanga da kuma arangama da jami’an tsro a birnin Addis Ababa. A kan wannan rikicin da kuma barazanar barkewar wani sabon yaki tsakanin Habashan da Eritrea ne wasu jaridun suka yi sharhinsu.

Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta dubi rikicin yankin kahon Afirka ne kamar wata guguwar iska mai karfi, wadda idan ta taso, barnar da za ta haddasa, zai yadu zuwa sauran yankunan nahiyar. Jaridar ta ce wani sabon mummunan yaki na barazanar barkewa tsakanin kasashen biyu, kwatankwacin dai na shekara ta 2000, inda aka yi asarar rayukan dimbin yawan jama’a, da sojoji da fararen hula. Yarjejeniyar da aka cim ma a Aljeriya a karshen shekara ta 2000, wanda aka ce za ta kawo karshen rikici tsakanin kasashen biyu, ba ta sami nasara ba. A daura da haka ma, rashin jituwa wajen aiwatad da wasu ka’idojin yarjejeniyar ne, tushen sabuwar hauhawar tsamarin da ake samu tsakanin mahukuntan birnin Addis Ababa da Asmara.

A lokacin kulla yarjejeniyar dai, Habasha ta dau alkawarin cewa, za ta amince da duk wani hukuncin da kwamiti mai zaman kansa da za a kafa, ya yanke, a kan tsara iyakokin kasashen biyu. To amma ga shi yanzu, ta ki cika wannan alkawarin.

Sabili da hakan ne kuwa, watakila Eritrean ma ta ki bin sauran ka’idojin yarjejeniyar ta birnin Algiers, tare da kin bai wa jami’an sa ido na Majalisar dinkin Duniya da aka girke a kan iyakar, damar gudanad da ikinsu yadda ya kamata.

Jaridar die tageszeitung ta yi sharhi ne kan makomar wasu `yan gudun hijira kimanin dubu 6 da ake niyyar kora daga Afirka Ta Kudu. Mafi yawan wadannan mutanen dai, inji jaridar, na da asali daga Zimbabwe da Mozambique. A halin yanzu, suna jibge ne a a sansanin `yan gudun hijiran nan na Lindela, inda mafi yawansu ke fama da rashin lafiya. Bugu da kari kuma, ba sa samun kyakyawar kulawa. Wasu rahotanni na nuna cewa, tsakanin watan Janairu zuwa Augusta na wannan shekarar, `yan gudun hijira 53 ne suka mutu a sansanin. Ana dai ganin cewa, da an kula da su a asibiti, da a kalla mutane 28 daga cikinsu ba su rasa rayukansu ba.

Bisa wani kiyasi, kusan `yan gudunn hijira miliyan 5 ne ke zaune a Afirka Ta Kudu a halin yanzu. Kuma, wannan sansanin na Lindela, shi ne dai matattarar `yan gudun hijiran. Duk inda aka kamo su, a nan ne ake kai su, kafin a debe su cikin jiragen kasa, a koma da su kasashensu, wato Mozambique da Zimbabwe. A shekarar bara kawai, inji jaridar, `yan gudun hijira dubu 67 ne aka kora daga Afirka Ta Kudun. A wannan shekarar kuma, kawo yanzu, an mai da `yan gudun hijira dubu 57 da dari 9 zuwa kasashensu.