1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Ra'ayoyin jaridun Jamus a kan nahiyar Afirka a wannan amkon.

A wannan makon ma, jaridun Jamus da dama ne suka duƙufad da wasu rahotanni da sharhohinsu kan nahiyar Afirka. A cikin batutuwan da suka fi jan hankullansu kuwa, har da batun garkuwan da ’yan ta kifen yankin Naija-Delta a tarayyar Najeriya ke yi da baƙi ma’aikatan haƙo man fetur, da yarjejeniyar da ƙasar Cadi ta cim ma da Bankin Duniya, a kan yin amfani da kuɗaɗen da take samowa daga kasuwancin man fetur da kuma yunƙurin da dakarun gamayyar kotunan islama na ƙasar Somaliya ke yi wajen yaƙan ’yan fashin jiragen ruwa a gaɓar tekun wannan ƙasa.

Mayaƙan gamayyar kotunan islama a birnin Mogadishu

Mayaƙan gamayyar kotunan islama a birnin Mogadishu

Da farko dai jaridar Süddeutsche Zeitung ta yi sharhi ne kan halin da ake ciki yanzu a yankin Naija-Delta, inda ake ta ƙara yin garkuwa da baƙi ma’aikatan kamfanonin haƙo man fetur a wannan yankin. Jaridar ta ce shugaba Olusegun Obasanjo na Najeriya ya yi barazanar sanya ƙafar wando ɗaya da ’yan ta kifen yankin. Ta ari bakinsa yana mai cewa „ko ina muka gano maɓuyar masu garkuwa da mutane, sai mun kau da su daga doron ƙasa.“ Jaridar dai ta ce, shugaban na ƙalubalantar masu garkuwan ne, don kada ya kasance kamar raggo a ganin masu sa ido a al’amuran da ke kai suna kawowa a ƙasar.

A yankin Naiija-Delta mai arzikin man fetur, inji jaridar, sai ƙara garkuwa da baƙi ma’aikatan haƙo man ake ta yi. A halin yanzu dai Jamusawa biyu na cikin waɗanda ake garkuwa da sun. Amma ma’aikatar harkokin wajen Jamus, ta ƙi tabbatad da rahotannin da ke nuna cewa an sako ɗaya daga daga cikin Jamusawan.

Jaridar ta ƙara da cewa, gwamnatin shugaba Obasanjo ta ɗau tsauraran matakan tsaro don fatattakar ’yan ta kifen. Jami’an tsaro za su dinga sintiri a yankin ne ba dare ba rana. Tashe-tashen hankullan da ake yi a yankin dai ya janyo koma bayan haƙo man fetur a Najeriyan da kashi 25 cikin ɗari, inji jaridar. Wannan kuwa, ba ƙaramar asara ba ce, idan aka yi la’akari da cewa Najeriya ita ce ta 8, a jerin ƙasashen da suka fi haƙo man fetur a duniya. A shekarar bara Najeriya ta sami kuɗaɗen shiga na kimanin dola miliyan dubu 45 a kasuwancin man fetur, inji jaridar Süddeutsche Zeitung.

A cikin nata sharhin, jaridar Frankfurter Rundschau ta waiwayi halin da ake ciki ne a ƙasar Cadi, bayan yarjejeniyar da ƙasar ta cim ma da Bankin Duniya game da yadda za ta dinga kashe kuɗaɗen da take samu daga kasuwancin man fetur. Da can dai an sami saɓani ne tsakanin gwamnatin Cadin da Bankin na Duniya. Kafin a fara haƙo man a Cadi, inji jaridar, sai da mauhukuntan ƙasar suka amince su yi amfani da kashi 85 cikin ɗari na kuɗaɗen shigar da za su samu daga harkar man wajen gina ƙasar da kuma aiwatad da shirye-shiryen kau da talauci a Cadin. Bisa wannan tsarin, da kamata ya yi ke nan ƙasar ta yi amfani da dola miliyan ɗari 2 da 45 wajen gina hanyoyi da makarantu da kafofin kiwon lafiya. Amma a ƙarshen shekara bara, sai majalisar ƙasar ta yi biris da wannan tsarin. Tana ganin kamata ya yi a ba da fiffiko wajen sayo wa rundunar sojin ƙasar makamai, don ta iya yaƙan ’yan tawayen da ke kutsowa daga Sudan. A kan wannan batun ne dai aka sami rashin jituwa tsakanin Bankin Duniyar da mahukuntan Cadin.

To yanzu dai, bisa dukkan alamu, an sasanta wannan rikicin, inji jaridar. An cim ma sabuwar yarjejeniya, inda Cadin ta amince ta yi amfani da kashi 70 cikin ɗari na kuɗaɗen shigar da ta samu daga kasuwancin man fetur ɗin, wajen yaƙan talauci. A ganin masu kula da inganta halin rayuwar jama’a, wannan wani cikas ne ga shirin samar da walwala ga al’umman ƙasar.

Kafin shekara mai zuwa ne ake sa ran gabatad da wani tsari na musamman, inda ƙasar Cadin da Bankin Duniya da kuma ƙungiyoyin kula da inganta halin rayuwar jama’a, za su yarje a kansa, don ya zamo kamar alƙibla na shirin yaƙan talauci a ƙasar. Kazalika kuma za a kafa wani kwamiti, wanda zai dinga sa ido kan yadda ake amfani da kuɗaɗem cinikin man fetur ɗin ƙasar. To sai dai, gamayar ƙungiyoyin sa kai ta ƙasar Cadin na bayyana mamakinta ga yadda Bankin Duniyar ta amince da shugaba Derby. A ganin ƙungiyoyin, inji jaridar, gwamnatin ƙasar romon baka kawai take yi ba tare da cika alkawura ba. Sabili da haka, kamata ya yi Bankin Duniyar ya yarje kan cewar ya gaza, wajen cim ma burinsa na asali, wanda a kan hakan ne ma aka fara aikin haƙo man fetur ɗin a Cadi.

Ita ko jaridar Neue Zürcher Zeitung ta mai da hankali ne kan yadda ababa ke wakana a halin yanzu a ƙasar Somaliya, inda ta ce mayaƙan gamayyar kotunan islama da ke jan ragamar al’amuran yau da kullum a birnin Mogadishu, sun fara ɗaukan matakan kare jiragen ruwan fararen hula da ke zirga-zirga a gaɓar tekun ƙasar, daga gungunan ’yan fashi. Jaridar ta ari bakin wani kakakin gamayyar, yana mai cewar mayaƙanta sun kame garin Harardere, mai nisan kimanin kilomita 400 a arewa maso gabashin Mogadishu, babban birnin ƙasar. Kafin kame garin dai, a nan ne madugun yaƙin nan Abdi Mohammed Afweyne ke da ramin kurarsa. Daga nan ne kuma shi da muƙarrabansa ke afka wa jiragen ruwa don yi musu fashi.

Tun ƙarshen watan jiya ne dai shugaban majalisar ƙoli ta gamayyar islaman, Sheikh Hassan Dahir Aweys, ya ba da sanarwar cewa mayaƙan gamayyar za su kame garin Harardere, don kawo ƙarshen fashin da ake yi wa jiragen ruwa a ƙasar ta Somaliya.

 • Kwanan wata 18.08.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvPh
 • Kwanan wata 18.08.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvPh