1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

RA'AYOYIN JAMA'A A ISRA'ILA DA YANKIN FALASDINAWA KAN TARON SHARM EL- SHEIKH.

Bisa dukkan alamu wata iskar sauyi na kadawa a yankin Gabas Tsakiya. Yarjejeniyar da Isra'ila da FFalasdinawa suka cim ma a Sharm el-Sheik na kasar Masar ta sami amincewar shugabannin kasashen duniya da dama dav kuma majalisar dinkin duniya.

Mahmoud Abbas zai gaisa da Ariel Sharon, a taron kolin da suka yi a Sharm el-Sheikh.

Mahmoud Abbas zai gaisa da Ariel Sharon, a taron kolin da suka yi a Sharm el-Sheikh.

"Babu wanda zai iya bai wa yaran nan wani uba kuma, bayan da aka halak ubansu. Kazalika ma, mace wadda ta rasa mijinta a wannan rikicin, babu wanda zai iya mayar mata da shi. Har ila yau, duk wasu lokutan annashuwa da shakatawa da suka wuce, babu abin da zai iya maye gurbinsu. Amma ina mai kyakyawar fatar cewa, wannan halin da na sami kaina a ciki, ba zai shafi mutane da yawa ba, kuma ina fatar ganin wannan shawarwarin wanzad da zaman lafiya da ake yi ya haifad da wani sakamako na zaman lafiya mai inganci."

Mai wannan bayanin dai, sunanta Tova Bahat. Bayahudiya ce a birnin Haifa. Tun shekaru biyu da suka wuce ne ta rasa mijinta, sakamakon wani harin kunan bakin waken da aka kai a wani gidan cin abinci a birnin na Haifa. Bayan taron kolin da aka yi a Sharm el-Sheikh, Tova na kyatata zaton cewa, yanzu dai za a kawo karshen wadannan kashe-kashen. Za a shiga cikin wani sabon zamani na zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya.

Ba dai dukkan Yahudawa a Isra’ilan ne ke da wannan raayi irin na Tova ba. A zangon masu bin ra’ayin mazan jiya, jama’a na ta kara nuna damuwar cewa, Falasdinawan za su iya yin amfani da wannan damar tsagaita bude wutar da suka samu, wajen sake cin damar kicin-kicin, kafin su fara wani sabon zagaye na kai wa Isra’ilan hare-hare kuma. Yahudawan share wuri zauna , na yankunan da Isra’ilan ta mamaye a zirin Gaza, sun fi nuna bacin ransu ga wannan yarjejeniyar da aka cim ma. Suna kuma ganin firamiyan Isra’ilan Ariel Sharon, ya kai su ne ya baro. Kamar dai yadda Shoshi Slutzki, wadda ke zaune a matsugunin kwarin Ganei, a kudancin zirin na Gaza ta bayyanar:-

"Lokacin da na ga shugaba Mubarak da Sharon suna dan takawa a gun taron Sharm el-Sheikh, a talabijin, sai na san cewa Sharon ya yi mana cin amana. Tun kafin hakan ma, ina da wannan ra’ayin. Mu ne dai muka taimaka wa Sharon har ya bunkasa, musamman ma mu `yan zirin Gaza. Da can ya kann ziyarce mu a ko yaushe, amma yau sai ga shi ko kallonmu ma ba ya yi. Ko sauraronmu ma bai yi ba, a lokacin da muka bukace shi ya shirya zaben raba gardama, don samun amincwar jama’a ga shirinsa na janyewa daga zirin Gaza."

To sai dai, ba a Isra’ilan kawai ne ake samun bambancin ra’ayi kan taron kolin da aka yi a Sharm el-Sheikh ba. A yankunan Falasdinawa ma, akwai masu fatan cim sakamako na gari, akwai kuma masu nuna shakkunsu ga duk shirin ma gaba daya. Har ila yau dai, mayakan kungiyoyin Falasdinawa daban-daban a zirin Gazan sun ce ba su amince da kwance musu damara ba. Ba su yi amanna da abin da suke gani kamar romon bakan da aka yi a taron kolin ba. Abu Mahmad, wani shugaban reshen kungiyar nan ta baraden al-Aqsa ne da ke arewacin zirin Gaza. A nasa ganin dai:-

"Har ila yau dai, ba mu zo ga karshen Intifadan ba tukuna. Ga alamu nan ko’ina, kuma ababa da dama na aukuwa, wadanda ke nuna cewa, mahukuntan Isra’ila ba sa kaunar ganin kawo karshen Intifadan balantana ma a zo ga tsagaita bude wuta."

A halin da ake ciki yanzu dai, mayakan wannan kungiyar da ke karkashin Abu Mahmad, suna ci gaba da atisayensu. Sun yi imanin cewa, yarjejeniyar tsagaita bude wutar da aka cim ma tsakanin Isra’ilan da Falasdinawa, ba za ta yi karko ba.

"Idan ya zamo tilas, za a sake samun hare-hare. Idan `yan bangaren Isra’ilan suka afka mana, za mu mai da martani. Wa ke da ikon hana aukuwar haka

? Zartad da kuduri kawai ko umarni ba zai iya hana aikata wani abu ba. Hare-haren da muke kai, wato mai da martani ne ga tsokana da kisan da Isra’ila ke ta yi wa al’umman Falasdinawa."

Sauran `yan ta kifen islama da ke zirin Gazan ma, ba su tabbatar cewa, an zo ga ketowar alfijir na wani sabon zamani ba. Duk da cewa, kungiyar Hamas ta nuna goyon bayanta ga shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas bisa manufa, ta kuma dau alkawarin kiyaye tsagaita bude wutar da aka cim ma, har ila yau da akwai kanan kungiyoyi kamarsu islamic Jihad, wadanda shawo kansu ke da wuya. Nafzam Asam, yana daya daga cikin shugabannin kungiyar Jihad din a zirin Gaza. Shi ma, ba ya ganin kawo karshen Intifada saboda cim ma wannan yarjejeniyar kawai:-

Intifada ba ta kare ba. Ba mu kawo karshen daddagewar mu ba tukuna. Idan muna zancen sassaucin tsamari a yankin, wato hakan ba ya nuna cewa, an kawo karshen Intifada da daddagewar ke nan."

Babu shakka, Mahmoud Abbas da Ariel Sharon na da gagarumin aiki a gabansu. A bangare daya, dole ne su iya shawo kan masu nuna shakku ga manufofinsu. Sa’annan a daya bangaren kuma, su taka wata rawar gani, don karfafa wa masu fatar barkewar wani sabon zamani na walwala da zaman lafiya, gwiwa.

 • Kwanan wata 09.02.2005
 • Mawallafi Yahaya Ahmed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvdJ
 • Kwanan wata 09.02.2005
 • Mawallafi Yahaya Ahmed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvdJ