1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ra´ayoyin jama´a a game da kissan Gebrane Tueni

December 13, 2005
https://p.dw.com/p/BvGh

Kasashe da kungiyoyi daban daban na dunia na cigaba da yin Allah wadai, da kissan gillar da yan ta´ada su ka yi wa Gebrane Tueni, dan majalisar Dokoki, kuma dan jarida a kasar Labanon.

A huruncidfa ta yi sakatariyar harakokinwajen Amurika Condolisa Rice ta tabatar da cewa Amurika tare da hadin gwiwa da sauran kasashen dunia za su bin diddikin wannnan kisan kai, su kuma kuma yi tsaye, sai an hukunta wanda wanda ke da hannu aciki.

Condolisa Rice, kamar iyalan mamacin, ta rataya alhakin kissan ga kasar Syria, tace lokaci yayi, da ta kamata Syria, ta tsame hannuwan ta kwata kwata,daga harakokin cikin gida na kasar Labanon.

Idan dai ba a manta ba, tun jiya, hukumomin Syria sun wanke kan su daga wannan zargi.

A yau ne kuma, Sakatare janar na Majalisar Dinkin Dunia Koffi Anan, zai karbi sakamakon binken da a ka gudanar, a game da kissan gilar da ya halla tsofan Praministan Labanon Raffik Hariri.