1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ra'ayoyin da jaridun Jamus suka buga kan nahiyar Afirka a wannan makon.

YAHAYA AHMEDAugust 5, 2005

Jaridun Jamus a wannan makon, sun fi mai da hankalinsu game da rahotanni da sharhohin da suka buga kan Afirka ne, a kan mutuwar da mataimakin shugaban kasar Sudan, John Garang ya yi, a hadarin jirgin sama mai saukar ungulu, a ran asabar da ta wuce. Sai kuma batun juiyn mulkin da aka yi a kasar Murteniya, wanda shi ma ya sami ambato a shafin farko na wasu jaridun. Har ila yau dai, wasu jaridun kuma, sun yi sharhi kan batun ba da taimakon agaji a nahiyar Afirka, ta yin la’akari da bala’in yunwar nan da ta auku a kasar Nijer.

https://p.dw.com/p/Bvp7
Jaridar "Berliner Zeitung"
Jaridar "Berliner Zeitung"

Jaridar die Tageszeitung, ta buga wani dogon rahoto da sharhi ne kan hadarin da ya ritsa da John Garang, tsohon shugaban kungiyar `yan tawayen SPLA, kuma mataimakin shugaban kasar Sudan. A ran asabar da ta wuce ne, inji jaridar, tsohon madugun `yan tawayen ya gamu da ajalinsa, yayin da jirgin sama mai saukar ungulun da yake ciki, ya yi karo da wani dutse a kudancin Sudan. Babu wanda ya tsira a hadarin. Bayan John Garang din, jirgin na kuma dauke da masu yi masa rakiya guda 6, da ma’aikta guda 7. Jaridar ta kara da cewa, bayan ba da sanarwar mutuwar mataimakin shugaban na Sudan ne, tashe-tahsen hankulla suka barke a birane da dama na kasar. A birnin Khartoum kawai, an sami arangama tsakanin larabawa da `yan kudancin Sudan din, inda aka sami asarar rayuka da dama. Sai da sojojin kasar suka yi katsalandan don kwantad da kurar rikici.

A halin yanzu dai, inji jaridar, mataimakin shugaban kungiyar SPLA din, Silva Kiir Mayardit ne zai gaji mukamin John Garang. A cikin farkon jawabin da ya bayar, bayan wani taron gaggawar da kungiyar ta yi a sansaninta da ke kudancin Sudan din, Silva Kiir, ya dau alkawarin bin sahun John Garang, da kuma cika alkawarin da ya dauka. Kazalika kuma ya ce zai yi kokarin kiyaye ka’idojin yarjejeniyar da kungiyarsa ta kulla a lokacin John Garang, da gwamnatin Sudan.

Jaridar Berliner Zeitung, ita ma ta yi sharhi ne kan tahse-tahsen hankullan da suka barke a Sudan bayan mutuwar John Garang. Bisa cewarta dai, yawan asarar rayukan da aka yi sakamakon wannan rikicin, ya tashi zuwa dari da 30. A birnin Khartoum kawai, mutane dari da 11 ne suka rasa rayukansu, inji jaridar, ta yin matashiya da bayanan da shugaban kungiyar agaji ta Sudan din, John Lobore, ya bayar. Jaridar ta kuma kara da cewa, an yi asarar rayuka a biranen Juba da Malakal a kudancin kasar. Larabawa da dama da ke zaune a birnin na Juba sun kaurace wa matsugunansu, saboda afka musu da `yan kudun ke yi. Mafi yawa daga cikinsu ma, sun bar yankin gaba daya, suna kaura zuwa arewacin kasar. Amma a halin yanzu, kurar rikici na lafawa, bayan da aka girke jami’an tsaro a kan muhimman titunan birnin, suna sintiri don hana `yan tarzoma ta da zaune tsaye.

Jaridar ta Berliner Zeitung dai, ta bayyana cewa, jirgin da John Garang ya yi hadari a cikinsa, bai cika duk ka’idojin kare lafiyar jama’a ba, a lokacin da ya tashi.

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta buga wani dogon rahoto da kuma sharhi ne kan juyin mulkin da aka yia kasar Murteniya a ran larabar da ta wuce. A cikin sharhinta kann juyin mulkin, jaridar ta ce:-

„A kasar Murteniya, hukumar soji ta adalci da dimukradiyya ta nada shugaban rundunar `yan sandan kasar, Ely Ould Mohammed Val, tamkar sabon shugaban kasa. Shi dai shugaban `yan sandan, wani dan hannun daman hambararren shugaba Mu’awiya Ould Sid Ahmed Taya ne.“

Jaridar ta kara da cewa, tuni, babban sakataren Majalisar dinkin Duniya Kofi Annan, ya yi kakkausar suka ga juyin mulkin da aka yi, da cewa, ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar ta Murteniya. Kazalika kuma, kungiyar Tarayyar Afirka da kungiyar Hadin Kan Turai, sun yi suka ga juyin mulkin. Jaridar ta kuma ce, gwamnatin Amirka, wadda, ke da kyakyawar hulda da hambararriyar gwamnatin ta Murteniya, ta yi kira ga maido da ita kan karagar mulki ta hanyar hannunka mai sanda.

A halin yanzu dai, inji Frankfurter Allgemeine Zeitung, sabuwar hukumar ta Murteniya ta ce, sai bayan shekaru biyu nan gaba ne za ta shirya zaben dimukradiyya don zaban sabon shugaban kasa.

Jama’a da dama sun yi ta bayyana murnarsu a birnin Nouakchott, babban birnin kasar murteniyan, bayana ba da sanarwar juyin mulkin da aka yi. Tsohon shugaban kasar Ahmed Taya, yana birnin Riyadh ne don halartar jana’izar sarki Fahad na Sudiyya, a lokacin da aka yi juiyn mulkin. A halin yanzu dai, yana zaman gudun hijira ne a birnin Yamai na kasar Nijer.

Jaridar Frankfurter Rundschau, ta yi sharhi ne kann tsarin shirye-shiryen ba da taimakon agaji a nahiyar Afirka, idan wata annoba ta kunno kai, kamar dai bala’in yunwar da ta yi tsamari a kasar Nijer, wadda take barazanar halaka kusan mutane miliyan 3 da digo 6.

Jaridar dai, ta yi kakkausar suka ne ga yadda gamayyar kasa da kasa ke zaman ba ruwanmu, game da matsalolin da ke kunno kai a nahiyar Afirka. Tun cikin watan Nuwamba ne, inji jaridar, Majalisar dinkin Duniya, ta yi gangami cewa, wani mummunan bala’i na shirin kunno kai a kasar Nijer, idan ba a dau matakai cikin gaggawa don bai wa kasar taimamon agaji ba. Amma babu abin da kasashe mawadata suka yi a wannan lokacin. A cikin watannin Maris da Mayu na wannan shekarar ma, sai da Majalisar ta sake neman taimako daga kasashe mawadata, amma ko rabin abin da take bukata ba ta samu ba. Sai da al’amura suka tabarbare, aka fara nuna hotunan yara kanana da ke mutuwa a tashoshin talabijin na kasashen duniya ne, kasashe mawadatan suka fara ba da taimako.

A daya bangarten kuma, jaridar ta Frankfurter Allgemeine Zeitung, ta yi suka ga shugaban kasar Nijer din, Tandja Mamadou, da yin sakaci da wannan matsalar da ta kunno kai a kasarsa. Ta ce, tun da aka gano a shekarar bara cewa, wannan matsalar za ta kunno kai, saboda ambaliyar fara da aka samu da kuma karancin ruwan sama, babu wani muhimmin matakin da shugaban ya dauka na tabbatad da cewa, an samar wa kasar, mai yawan jama’a kusan miliyan 13, wani shiri na tanadin isashen abinci. Duk da cewa kasar ta Nijer, na daya cikin mafi talauci a duniya, shugaban bai yi amfani da matsayinsa wajen nemna taimamko ba. A lal misali, jaridar ta ce, a lokacin da ya halarci taron rukunin kasashen G-8, a Gleneagles a Scotland, inda aka yafe wa Nijer basussukanta, ko ambatar batun yunwar ma bai yi ba, ballantana neman taimako. Da a nan ne ma kuwa, ya kamata shugaban ya yi gangami da kira ga neman taimakon. Har ila yau dai, inji jaridar, a lokacin da shugaba Tandja Mamadou ya kai ziyara a fadar White House a birnin Washington, bai tabo wannan batun ba a lokacin shawarwarinsa da shugaba Bush. Gwamnatin Nijer din kuma, ba ta yi wata wata ba, wajen daukan matakan rufe bakin duk wadanda suka yunkuri kawo wannan batun a bainar jama’a, kamar dai `yar jaridar nan ta Sahel, jaridar da ke karkashin ikon gwamnatin, wadda ta buga rahoto kan barkewar wannan annobar don janyo hankullar jama’a a kanta. Kai tsaye aka dakatad da ita daga aiki.

Ashe kuwa ba abin mamaki ba ne, inji Frankfurter Allgemeine Zeitung, da `yan adawar kasar ke zargin shugaba Tandja Mamadou, da samun hannu a tabarbarewar al’amura game da wannan bala’in yunwar a kasar ta Nijer.