Ra´ayoyi a game da ƙudurin MDD na aika dakaru a Darfur | Labarai | DW | 01.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ra´ayoyi a game da ƙudurin MDD na aika dakaru a Darfur

Bayan wata da wattani a na tabka mahaurori,jiya ne komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia, ya kaɗa ƙuri´ar amincewa da tura tawagar kwantar da tarzoma, a yankin Darfur na ƙasar Sudan.

Rundunar ta haɗin gwiwa, da aka raɗawa suna Unamid, za ta ƙunshi jimilar sojoji da yan sanda dubu 26, na Majalisar Dinkin Dunia, da ƙungiyar tarayya Afrika.

A na sa ran aika wannan runduna a farko watan janairu na shekara mai kamawa, wato kimanin shekaru 5 kenan, bayan ɓarkewar rikicin Darfur.

A yayin da ta ke maida martani, ƙasar Sudan ta yi lale marhabin da wannan ƙuduri, tare da fatan zai taimaka, wajen kawo ƙarshen rikicin.

Ƙungiyar tarayya turai, Amurika da Sin, dukkan su sun bayyana gamsuwa, saidai ƙasar Sin, ta yi hannu ka mai sanda, tare da cewar ya wajibi a yi takatsantan, wajen gudanar ayyukan wannan runduna.

Ƙasar duk da cewar ta bayyana gamsuwa da ɗaukar wannan mataki ,ta bayyana cewar, akwai matuƙar wuya, ta bada gudummuwar sojoji , a cikin wannan runduna.