RAAYIN SHUGABANNI GWAMNATOCI DA ADDINAI KAN SABON PAPAROMA. | Siyasa | DW | 20.04.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

RAAYIN SHUGABANNI GWAMNATOCI DA ADDINAI KAN SABON PAPAROMA.

RATZINGER:PAPAROMA BENEDICT XVI.

RATZINGER:PAPAROMA BENEDICT XVI.

MOD.:Shugabannin Gwamnatoci,da addinai da akasarin yan darikar roman katholika kimanin biliyan daya da digo daya,dake sassa daba daban na duniya sunyi maraba da zaban Joseph Ratzinger a matsayin paparoma Benedict na XVI,kodaya yake masu sassaucin raayi na darikar sun bayyana cewa babu wani sauyi da zaa samu.

Ana yiwa Sabon paparoman mai raayin rikau kuma bajamushe kallon cigaba ne daga inda tsohon paparoma marigayi John Poul na biyu ya bari,musamman amatsayinsa na daya daga cikin na hannun daman marigayin.

Manazarta da masu lura da alamura daka je suzo na ganin cewa babu shakka zaa cigaba da samun zaman lafiya tsakanin addinai daban daban na duniya.

Shugaba George W Bush na Amurka ya bayyana RatZinger,da kasancewa ,mutum mai dunbin ilimi,basira da hangen nesa,ayayinda sakatare general na mdd Kofi Annan yace ko shakka babu zaiyi amfani da wannan matsayi nashi wajen inganta cigaba.

Shugaba Horst Koehler na Jamus, ya kasa bayyana farin cikinsa dangane da zaban bajamushe na farko cikin shekaru dubu da suka gabata a matsayin Paparoma,wanda yace hakan abun alfahari ne wa jamusawa baki daya.

Shugabannin Musulmi da na Yahudawa a hannu guda sunyi fatan cewa Ratzinger mai shekaru 78 da haihuwa zai bi sawun marigayi Paparoma John Poul II,wajen cigaba da gyara danganta da banbanci da ake fuskanta tsakanin addinai.

To sai dai a bangare guda fatan da wasu keyi na ganin cewa an samu sassauci cikin dokokin darikar ta fannin yan luwai,mutuwan aure,limancin mata da shan kwayoyin dake hana haihuwa, ya dakushe.Masu sassaucin raayi na Darikar Katholika sun bayyana cewa basuyi fatan samun mutun kamar Ratzinger a matsayi paparoma ba. Joelle Battestini dake kungiyar nadin mata na darikar Katholika dake Australia,na mai raayin cewa ko kadan basuyi fatan Ratzinger a matsayin Paparoma ba.Ayayinda Matt Foremane dake hukumar lura da maza yan luwai da mata yan madigo,dake da zama a Amurka,yace tun kafin samunsa wannan matsayi Bajamushen ya sha bayyana kiyayyarsa wa yan Luwai.

Shi kuwa Direktan hukumar dake tabbatar sassauci dangane dangantakatar Addinai wanda kenan jamus Bernd Goehring,bayyana wannan zaben yayi da kasancewa balai.domin injishi basa tsammani wani sauyi acikin shekaru masu gabatowa,domin mutane da yawa zasu juyawa wannan majamia baya.

A yayinda ake fatan cewa Ratzinger zaiyi gagarumin jagoranci,wasu na masu raayin cewa bashi da kwar jinin marigayi Paparoma John Poul.Amma Archbishop na Canterbur,wanda ke jagorantan Anglikan kimanin million 70 a duniya,Rowan Wiilliams,ya yabawa wannan zabi da akayi,inda yayi alkawarin bashi hadin kai cikin dukkan ayyukansa da zai gudanar.Shi kuwa Rabbi David Rasen ,wanda ke zama directan komitin dangantakar yahudawa da wasu addinai dake Amurka.yace tuni sabon Paparoma na nuna hazaka wajen inganta dangantakar yahudawa da yan darikar katholika

Duk dacewa kasashen dake latin Amurka sun nuna adawa da zaban Ratzinger wadanda ke fatan daga nan ne zaa zabi sabon Paparoma,Shugaba Luiz Lula da Silva na Brazil,kasar dake dauke da mafi yawan yan Darikar katholika a duniya,yayi fatan cewa sabon Pasparoman zai taka rawar gani wajen kawo hadin da zamantakewa tsakanin alummomin darikar.Duk dacewa ratzinger bashi da kwarjin Marigayi John Poul ,Dan uwansa Georg Ratzinger yace yana da saukin kai na aiki dashi.

Zainab A Mohammed.