Ra′ayin Musulmi a game da sabon Paparoma | Siyasa | DW | 20.04.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ra'ayin Musulmi a game da sabon Paparoma

Kasashen Musulmi na duniya sun bayyana gamsuwarsu da sabon Paparoma Benedict XVI da aka zaba domin jagorantar mujami'ar katolika

Paparoma Benedict XVI

Paparoma Benedict XVI

Cardinal Joseph Ratzinger,Bajamushe mai raayin rikau ,wanda ya gaji Paparoma John Poul na II,a matsayin shugaban Darikar Roman Katholik a jiya talata ,ya haye wannan matsayi a daidai lokacin da ake fuskantar karuwan sabanin raayi tsakanin kasashen dake da rinjayen kristoci da kuma duniyar musulmi.

A dangane da hakane wani fitaccen limami kuma masani kann harkokin da suka jibanci siyasa a Pakistan, Hafiz Hussain Ahmedyayi fatan cewa sabon Paparoman zaiyi koyi da hali da dabiun marigayi.Ratzinger ya gaji wannan matsayi daga Marigayi John Poul,mutuminda duniyar musulmi dana yahudawa ke cigaba da darajawa har bayan mutuwansa.Shugabannin gwamnatoci daga bangarorin biyu sun halarci janaizarsa.

Sai dai wasu musulmi na ganin cewa saboda akidojinsa,sabon Paparoman bazai cimma wata kafa ba wajen hade gibin da addinan biyu ke cigaba da fuskanta.

Alal misali Shekh Ahmed yace akwai babban danuwa tsakanin alumman musulmi a dangane da yaki da ayyukan taaddanci da aka kaddamar yan shekaru da suka gabata.Yayi fatan cewa sabon Paparoman zai juya wannan akida da turai ta dauka dangane da duniyar musulmi.

Duniyar musulmi ta nuna bacin ranta wa shugaba George W Bush na amurka ,tun bayan harin 11 ga watan satumba na 2001,wanda daga nan ne ya kaddamar da yaki da ayyukan taaddanci ,musamman kann musulmi masu tsattsauran raayi.Tunda wannan loikaci ne Musulmi suka fara kallon tsohon Paparoma da kima,saboda kokarinsa na yaki da akidar zalunci ,ba tare da laakari da matsayin siyasa ba,tare kuma da fitowa dayayi karara ya nuna goyon bayansa wa fafutukar da Larabawan Palasdinu keyi na samun yancin kai,kana a hannu guda da nuna adawa da harin Amurka ta afkawa Iraki dashi a shekara ta 2003.Shine Paparoma na farko daya taka kafarsa cikin masalci,wanda kuma ke zama babban tarihi.

Indonesia,kasar dake dauke da mafi yawan alummar musulmi a duniya,tayi fatan cewa kusantaka dake tsakanin Ratzinger da marigayi John Poul zai taimaka matuka gaya wajen dorewar akidar zamantakewa tsakanin addinai,ata bakin Shekh Masduki Baidlowi.Shi kuwa Wakilin majalisar malamai ta Indonesia Maaruf Amin,shawara ya bawa sabon Paparoman daya dora daga inda ya tarar,koma yayi fiye da yadda ake kyautata zato.

Shi kuwa rime ministan Yemen Abubakar al-Qirbi fadawa manema labarai yayi cewa,yana fatan Ratzinger zai tsaya tsayin daka wajen kawo hadin kai tsakanin musulmi da Kristoci na duniya.Ayayinda Prime minister Abdullahi Ahmad Badawi na Malasia yayi kira ga ga musulmi baki daya dasu bada hadin kansu wa Paparoma Benedict na XVI,domin hadin kann addinan biyu.

Kristoci da Musulmi na masu zama rabin yawan alummomi na duniya .Ayanzu haka dai Paparoma Benedict ya gaji babban nauyi daya rataya a wuyansa,inda Musulmi da christocin ke fatan zai sauke su cikin adalci da gaskiya.