Ra′ayin masana game da ziyarar Obama a Ghana | Siyasa | DW | 13.07.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ra'ayin masana game da ziyarar Obama a Ghana

Masana da masharhanta na ci gaba da mai da martani dangane da ziyarar da shugaban Amirka Barack Obama ya kai a ƙasar Ghana.

default

Barack Obama a Ghana

Babban abin da ya fi ɗaukara hankalin jama'ar shi ne kiran da ya yi ga ƙasashen Afirka da su kare mulkin dimokuraɗiyya tare da gudanar da shugabanci na gari da kuma gujewa canja kundin tsarin mulki domin cimma wata buƙata. Kusan dukkanin jawaban da shugaba Obama gabatar a ƙasar Ghana, ba su zo wa mutane a bazata ba, domin kuwa dama an tsammaci hakan, musamman ma dai yadda ya nunawa al'ummar nahiyar Afirka cewa, makomarsu fa tana hannunsu, kuma dagewarsu akan ci gaban rayuwar al'ummarsu, shi ne abin da zai haifar da zaman lafiya da ci gaba a nahiyar ta Afirka.

Farfesa Johnson, mai ba da shawara ne ga shugabar majalisar zartarwar tarayyar Afirka, ya kuma bayyana cewar, abin da shugaba Obama ya ke nufi da makomar al'ummar Afirka tana hannunsu, shi ne cewar, tsarin da shugabannin Afirka ke kai na bara da roƙo da kuma kiran kullum a taimake su, dole ya tsaya hakanan, kuma duk wani tsari da za a yi nan gaba, ya zama wajibi ya zamanto akan tsarin cuɗanni in cuɗeka.

Barack Obama und John Atta Mills in Ghana Afrika

Barack Obama na Amirka da John Atta Mills na Ghana

Shi kuwa Dirk Kohnert wani jami'i ne a wata cibiya ta nazarin al'amuran Afirka da ke birnin Hamburg a nan Jamus. Ya bayyana abin da yake ganin shi ne saƙon da Obama yake ƙoƙarin isarwa ga al'ummar Afirka. yana mai cewa; "Idan kai nazarin jawabin Obama wani saƙo ne yake aikewa ƙasashen Afirka a matsayin sa na Ba'amurke ɗan asalin Afirka da ya zamo shugaban Amirka na farko. Kuma abin da yake nuna musu shi ne, babu wata ƙasa da za ta ci gaba a duniya, matuƙar dai shugabanninta suna yin amfani da tattalin arzikin ƙasa domin arzurta kansu kaɗai mai makon biyan buƙatun jama'a. Kuma wannan batu nasa gaskiya ne".

A ziyararsa ta farko ga ƙasashen Afirka da ke yankin hamadar Sahara, Obama ya tabbatar da asalinsa a matsayin ɗan asalin ƙasar Kenya, to amma kuma ya bayyana dalilinsa na ƙin zaɓar kenya ɗin domin ya kai ziyar farko zuwa gare ta. kamar yadda Kohnert yai martani akai yana mai cewa; " Obama Ya zaɓi Ghana ne daga cikin ƙasashen Afirka saboda ƙasar da iyayensa suka fito wato Kenya, ta yi dumu-dumu cikin harkokin cin hanci da rashawa da kuma rashin gudanar da mulki yadda ya kamata daga ɓangaren shugabannin da suke mulkin ƙasar".

Obama in Ghana

Barack Obama da iyalansa ana yi musu rawar gargajiya a Ghana

To sai dai duk da haka Kohnert ya yi hannunka mai sanda ga shugaba Obama, yana mai nuna cewa ai idan aka bi diddigin tarihi, Amirka na da hannu a lalacewar al'amura a nahiyar Afirka, don haka ya yi nuni da cewa, ya kamata idan ana ta ɓarawo to a riƙa yin ta mabi sawu. Inda ya ƙara da cewa; "Babban abin da Obama ya manta da shi, shi ne cewar, Ita kanta ƙasar Amirka ta taimaka wajen tabbatuwar mulkin kama-karya a nahiyar Afirka a kimanin shekaru 30 da suka gabata, misali tsohuwar ƙasar zayar da kuma Jamhuriyar Kongo inda hukumar leƙen asiri ta Amirka wato CIA ta taimaka wajen kashe shugaban ƙasar da aka zaɓa a wancan lokaci da dai sauransu".

Masharhanta da dama dai na ganin cewa, wannan ziyar ta Obama a ƙasar Ghana da kuma jawaban da ya yi, alamune da ke nuna sabon salon da Amirka ke shirin ɗauka na manufofinta akan ƙasashen Afirka, matuƙar dai suka dage wajen tabbatar da ingantacciyar Dimukuradiyya.