Ra´ayin Jaridun Ketare a al´amuran Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 29.09.2003
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Ra´ayin Jaridun Ketare a al´amuran Jamus

To sharhunan da jaridun ketaren suka yi dangane da al´amuran siyasar Jamus sun ta´allaka ne akan ganawar da aka yi tsakanin shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder da shugaban Amirka GWB a birnin New York, sai kuma gagarumar nasarar da jam´iyar CSU ta samu a zaben shiga majalisar dokokin jihar Bavariya a karshen makon jiya. A cikin shrahin da ta rubuta jaridar KOMMERSANT ta kasar Rasha ta bayyana taron da aka yi tsakanin Schröder da Bush da cewa abu ne mai muhimmanci, ba kawai kasancewarsa shine na farko cikin watanni da dama tsakanin shugabannin ba, a´a dinke barakar da ke tsakaninsu ya zama wani muhimmin sako ga duniya baki daya. Jaridar ta ce yanzu Jamus ta bi sahun Rasha wajen warware rashin jituwa dake tsakaninta da Amerika, kasar da ba ta yi hakan ba ya zuwa yanzu ita ce Faransa. A wani sharhi da ta rubuta jaridar LE MONDE ta Faransa ta fara ne da cewa in dai ana batun Iraqi ne to gwamnatocin biranen Paris da Berlin sun fara nuna sassauci a matsayinsu na adawa da yakin Iraqi. Jaridar ta ce Jamusawa na ganin nahiyar Turai ta yi rauni dangane da wannan matsayin, domin Jamus ta kasa iya taka rawar ´yar shiga tsakanin gwamnatocin Paris da Washington. To sai dai ganawar da aka yi tsakanin Bush da Schröder wani babban ci-gaba ne da bai kamata a yi watsi da shi ba.
Ita kuwa jaridar DER STANDARD ta kasar Austria ta yi sharhi ne kamar haka: Sassaucin da Schröder ya yi ga matsayin sa na farko, wato na kusantar shugaba Bush sannan a daya hannun ya dan fara nesanta kanshi da shugaba Chirac zai karfafa manufofinsa na ketare. To amma jaridar ta ce sai da a jira a gani ko wannan matakin da Schröder ya dauka zai amfanad da Jamus na lokaci mai tsawo. To duk da haka dai abin da ke a fili shine Jamus na kara sanin inda ta dosa a manufofinta na ketare.
To sai dai ka da Schröder ya wuce makadi da rawa, inji jaridar DE VOLKSKRANT ta kasar Netherlands.
Ita kuwa jaridar LA REPUBLICA ta birnin Rom ta yi sharhi ne dangane da zaben shiga majalisar dokokin jihar Bavariya, inda jam´iyar CSU ta samu gagarumin rinjaye. Jaridar ta ce sakamakon wannan zabe wani sako ga gwamnatin hadin guiwa ta SPD da Greens, cewa al´umar kasar sun fara kosawa da manufofin gwamnati. Ita ma jaridar ABC ta kasar Spain ta goyi da bayan ra´ayin jaridar Le Republica cewa Edmund Stoiber ya jagoranci jam´iyar CSU a jihar Bavariya, wajen lashe kashi biyu cikin uku na kuri´un da aka kada, wanda hakan ya kasance na farko a cikin tarihin Jamus tun bayan yakin duniya na biyu.
Jaridar FINANCIAL TIMES ta Britaniya ta bayyana sakamakon wannan zabe ne da cewa babbar nasara ce ga Firimiyan jihar Bavariya Edmund Stoiber. Jaridar ta ce bayan ya sha kaye a zaben shiga majalisar dokoki ta Bundestag a bara, jama´a ta kusan mantawa da shugaban na jam´iyar CSU, amma bisa ga dukkan alamu yanzu yana iya dawowa a matsayin dan takarar jam´iyun CDU da CSU a zaben majalisar dokoki na shekara ta 2006.
To jama´a karshen sharhunan da jaridun kasashen ketare suka rubuta kenan dangane da Jamus. Jamila gareki.


 • Kwanan wata 29.09.2003
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvqV
 • Kwanan wata 29.09.2003
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvqV