Ra′ayin jaridun Jamus kan nahiyar Afirka a wannan makon. | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 29.07.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Ra'ayin jaridun Jamus kan nahiyar Afirka a wannan makon.

Batun annobar yunwa da ke barazanar addabar dubun dubatan jama'a a kasashen yammacin Afirka, da rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta buga kan kasar Zimbabwe, game da rusa gidajen dimbin yawan jama'a a kewayen birnin Harare da gwamnatin shugaba Robert Mugabe ta sa aka yi, na cikin muhimman jigogin da suka shafi nahiyar Afirka, wadanda kuma jaridun Jamus suka yi sharhi a kansu a wannan makon.

Jaridar Frankfurter Rundschau, daya daga cikin muhimman jaridun Jamus

Jaridar Frankfurter Rundschau, daya daga cikin muhimman jaridun Jamus

Rikice-rikice da bala’o’i da ake ta fama da su a nahiyar Afirka, su ne dai, kamar a galibin lokuta, suka fi jan hankullan mafi yawan jaridun Jamus a sharhohi da rahotannin da suka buga kan nahiyar a wannan makon. Jaridu da dama sun yi sharhi ne kan rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta buga game da rushe matsugunan dubannin marasa galihu da ke zaune a kewayen birnin Harare na kasar Zimbabwe. Wasu jaridun kuma, sun takalo batun yaduwar annobar yunwar ne a kasashen Afirka Ta Yamma. Ban dai kasar Nijer, yanzu bala’in na barazanar halaka dimbin yawan jama’a ne kuma a kasashen Mali, da Burkina Faso da Murteniya.

To da farko dai, jaridar die Tageszeitung, ta yi sharhi ne kan rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta buga game da rusa gidajen dimbin yawan marasa galihu, da gwamnatin shugaba Robert Mugabe na kasar Zimbabwe ta sa aka yi, a kewayen birnin Harare, babban birnin kasar. Rahoton dai, inji jaridar, ya ba da mummunan sakamako ne da wannan matakin ya janyo wa dubun dubatan jama’a a kasar. Jaridar ta kara da cewa:-

„Abin ban takaici ne dai a ce wani shugaban kasa ya gallaza wa mutane fiye da dubu 70, `yan kasarsa, wai kawai saboda daukar fansa game da kin ka da masa kuri’u da suka yi. Idan dai wannan zargin gaskiya ne, to lalle gwamnatin shugaba Mugabe ta cancanci a sanya mata takunkumi. Rahoton Majalisar Dinkin Duniyar, ya ce dimbin yawan mtane, maza da mata da yara ne wannan matakin ya shafa, inda a halin yanzu ba su da matsugunai kuma, balantana ma a yi zancen samar musu ruwan sha mai tsabta ko kuma cibiyoyin kula da lafiyarsu. Bugu da kari kuma, wadanda abin ya fi shafa, wato talakawa ne na can kasa kasa, na al’umman kasar.“

Jaridar Frankfurter Rundschau kuma, ta yi sharhi ne kan bala’in yunwar da ke addabar wasu kasashen yankin Sahel a yammacin Afirka. Tuni dai, inji jaridar, ta yin matashiya da wasu alkaluman da Majalisar dinkin Duniya ta buga, annobar ta ritsa da dubban yara a kasar Nijer. Kazalika kuma, tana yaduwa zuwa wasu kasashen da ke makwabtaka da Nijer din, musamman ma dai Mali, da Burkina Faso da kua Murteniya, inda a halin yanzu, kusan mutane miliyan biyu da rabi ne take barazanar halaka su, idan ba su sami taimako a kan lokaci ba.

Game da tafiyar hawainiyar da kasashe mawadata ke yi wajen ba da taimako ga kasashen Afirka dai, jaridar ta Frankfurter Rundschau ta ce, sai bayan al’amura sun tabarbare matuka ne jiragen sama dauke da kayan taimakon agaji daga ketare suka fara sauka a birnin Yamai, na kasar Nijer. Ko fara sauke kayan ma ba a yi ba, sai ga shi kuma Hukumar Ciyad da Duniya da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, tana gangamin cewa, anobar fa na barazanar ritsawa da dimbin yawan jama’a a kasashen da ke makwabtaka da Nijer din.

A kasar Mali kawai, inji jaridar, kusan mutane miliyan daya da digo daya ne suka dogara kan taimakon abinci a halin yanzu daga kafofin Majalisar Dinkin Duniya. Ta kuma ari bakin babban jami’in Majalisar mai kula da tsara shirye-shiryen ba da taimakon agaji, Jan Egeland, yana mai cewar, yawan yaran da ke mutuwa a wasu yankunan kasar ya habaka a kwanakin bayan da suka wuce. Amma jami’in ya kuma bayyana cewa, bayan yada hotunan da aka yi a kan talabijin din kasashen duniya, na ramammun mutane da yunwar ke addabarsu da kuma yaran da ke mutuwa a kasar Nijer, an yi ta samun karin yawan alkawarin taimako a lokaci daya, wadanda a cikin watanni goman da suka wuce, ba a same su ba. Sai dai, alkawari ne kawai da aka yi amma ba a cika ba su tukuna. Kawo yanzu dai, Majalisar Dinkin Duniya, ta ce kashi 20 cikin dari kawai ta samu na kimanin Euro miliyan 30 da ta ce ana bukata don tinkarar matsalar yunwar a kasar Nijer. Tun shekarar bara ne dai Majalisar ta yi ta gangamin cewa, wani bala’i na barazanar kunno kai a yankin na Sahel, amma ko kulawa da batun, kasashe mawadata ba su yi ba, sai da matsalar ta kai ta kawo tukuna.

Jaridar Die Zeit, ta buga rahoto ne kan wani sabon rikicin da ke niyyar barkewa a kasar Côte d’Ivoire. Wasu hare-haren da `yan bindigan da ba a gano asalinsu ba tukuna, suka kai kan yankunan da ke hannun dakarun gwamnati, sun sa bangarorin biyu, na`yan tawayen da na gwamnatin Côte d’Ivoire din sun ja damara da shirin ko ta kwana. Tuni dai gwamnatin shugaba Laurent Gbagbo na zargin`yan tawayen ne da kai hare-haren. Su ko `yan tawayen, wadanda su ne a yanzu ke rike da yankunan arewacin kasar, tuni sun yi watsi da wannan zargin.

Hauhawar tsamarin da ake samu a kasar ta Côte d’Ivoire a halin yanzu, ta zo ne a daidai lokacin da ake shirye-shiryen kwance wa bangarorin biyu damara, kafin a gudanad da zabe a cikin watan Oktoba mai zuwa, karkashin yarjejeniyar da suka cim ma a birnin Pretoria na kasar Afirka Ta Kudu.

 • Kwanan wata 29.07.2005
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvp8
 • Kwanan wata 29.07.2005
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvp8