Ra′ayin Jaridun Isra′ila game da yakin Lebanon | Siyasa | DW | 20.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ra'ayin Jaridun Isra'ila game da yakin Lebanon

A yayinda wasu jaridun Isra'ila ke goyan bayan yakin wadansunsu kuma sukan lamirin gwamnati suke yi

Yakin Lebanon

Yakin Lebanon

A cikin sharhin da ta gabatar jaridar Jerusalem Post ta bayyana cewar al’umar Lebanon na fama da radadi sakamakon taimakon da gwamnatin kasar ke ba wa kungiyar Hizbullah. Ta jaridar ta kara da cewar:

“A hakika ba mai fatan hakan ya faru, amma fa har yau jami’an diplomasiyyar kasar Lebanon na kare hakkin kungiyar Hizbullah na gwagwarmaya da sojan mamaye, kamar dai kasar Isra’ila dama tana da mamaye ne da wani yanki na kasar kafin Hizbullah ta kai wa sojojinta hari. Abin dake akwai shi ne ba tabbas ko gwamnatin Isra’ilar zata tinkari Hizbullah idan Isra’ila ta dakatar da hare-harenta, domin kuwa kungiyar na da wakilci a majalisar ministocin gwamnatin. A sakamakon haka dukkan Isra’ilawa ke ba da goyan baya ga manufar murkushe Hizbullah ko ta halin kaka da kuma wani tabbaci daga Lebanon game da cewar zata zata cika alkawururrukanta.”

Ita kuwa jaridar Yedioth Ahronoth da ake bugawa da turanci a Isra’ilar ta dubi matakan gwamnatin ne da idanun musu tana mai cewar:

“Isra’ila ba tayi hangen nesa ba. Kasar tayi shekara da shekaru tana mai watsi da muhimmancin rarrashi da neman goyan baya daga ainifin talakawan Palasdinu ta yadda zasu bijire wa kungiyoyi masu zazzafan ra’ayi na akida. A maimakon haka sai ta bi wata manufa ta buge-ni-in-buge-ka da kuma ramuwa ta gama gari ba tare da banbanta masu laifi da marasa laifi ba.”

Dangane da jaridar Haaretz mai fita kullu yaumin kuwa, masharhantanta sun fi mayar da hankali ne tare da saka ayar tambaya ko Ya-Allah yaushe Allah zai nuna musu karshen wannan mataki na soja:

“Akwai hanyoyi da dama na kawo karshen wannan yaki, ko dai ta halaka madugun kungiyar Hizbullah Nassrallah da murkushe sauran shuagabanninta ko kuma karya alkadarin reshen soja na kungiyar ta yadda ba zasu samu ikon ci gaba da hare-harensu na rokoki ba. Hakan ba shakka zai taimaka gwamnatin Lebanon ta sake samun cikakken ikonta. Amma fa da wuya a cimma wannan buri. Daya hanyar kuma ita ce ta shiga tattaunawa tare da ci gaba da fafata yakin, ko kuwa a cimma wata daidaituwa ta tsagaita wuta wadda zata zama madogarar wata babbar yarjejeniya tare da gwamnatin Lebanon. Idan matakan na diplomasiyya ba su cimma nasara ba ko kuma matakan na soja ba su tsinana kome ba, wani bangare na iya ikirarin tsagaita wuta na radin kasa domin ya dakaci martanin da daya bangaren zai mayar.”