Ra′ayin Jami′an Siyasar Jamus Game Da Rasuwar Arafat | Siyasa | DW | 11.11.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ra'ayin Jami'an Siyasar Jamus Game Da Rasuwar Arafat

A martanin da suka mayar dangane da rasuwar shugaban Palasdinawa Malam Yassir Arafat jami'an siyasar Jamus sun bayyana fatan samun ci gaba a fafutukar sasanta rikicin Yankin Gabas ta Tsakiya

Marigayi shugaba Yassir Arafat

Marigayi shugaba Yassir Arafat

Babban abin da jami’an siyasar Jamus ke fata dangane da rasuwar shugaban Palasdinawa Malam yassir Arafat shi ne cewar sabbin shuagabannin Palasdinawan zasu cimma nasarar sake dora shawarwarin sasanta rikicin Yankin Gabas ta Tsakiya akan wata hanya madaidaiciya. Shugaban kasar Jamus Horst Köhler ya ce yana sabbin shuagabannin Palasdinawa fatan alheri da kuma karfin hali wajen bin wata nagartacciyar hanyar da zata kai ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma garambawul ga manufofin Palasdinu. A nasa bangaren shugaban gwamnati Gerhard Schröder nuni yayi da gwagwarmayar da marigayi Malam Arafat ya sha famar yi tsawon rayuwarsa a fafutukar samarwa da Palasdinawa cikakken ‚yanci da walwala a karkashin tutar wata kasa tasu ta kansu. Shi kuwa ministan harkokin waje Joschka Fischer cewa yayi rayuwar Arafat abu ne dake tattare da bakin ciki da tausayi ga tarihin Palasdinawa. A cikin rahotonsa game da majalisar shawara ta ministocin harkokin wajen kasashen Kungiyar Tarayyar Turai Joschka Fischer ya fada wa majalisar dokoki ta Bundestag cewar:

Muddin ba wani sahihin ci gaba na a zo a gani aka samu a shawarwarin zaman lafiyar Yankin Gabas ta Tsakiya ba to kuwa babu yadda za a yi a shawo kan sauran rikice-rikicen dake addabar shiyyar. Shirin Isra’ila na janyewa daga zirin Gaza da wani bangare na yammacin gabar kogin Jordan wata dama ce ta samun ci gaba a shawarwarin sulhun, wadda ya kamata a yi amfani da ita. Wani muhimmin abu a yanzun, bayan mutuwar shugaba Arafat, shi ne kada a samu gibin shugabanci a kuma nada magajinsa a cikin gaggawa ba tare da jinkiri ba.

To sai dai kuma an saurara daga bakin kakakin jam’iyyar SPD akan manufofin ketare Friedbert Pflüger yana mai kokarin tunasarwa da cewar ko da yake ana danganta sunan Arafat da yarjejeniyar Oslo ta zaman lafiya, amma fa ka da a manta da nasabta shi da ake yi da ta’addancin Palasdinawa, wanda ya salwantar da rayukan dubban mutanen da ba su san hawa ba, ba su kuma san sauka ba.