Ra′ayin Jami′an Jamus A Game da Zaben Amurka | Siyasa | DW | 03.11.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ra'ayin Jami'an Jamus A Game da Zaben Amurka

Akwai dai banbance-banbancen matsayi a tsakanin jami'an siyasar Jamus dangane da zaben kasar Amurka, ko da yake gaba daya sun hakikance cewar babu wani banbancin da za'a samu a dangantakar kasashen biyu tare da kowace gwamnati ce za a nada nan gaba a fadar mulki ta White House

A hakika dai babu wani canjin da za a samu a dangantakar Jamus da Amurka Ya-Allah Bush ne ya lashe zaben ko abokin takararsa John Kerry, wannan shi ne martani na farko da jami’an siyasa a fadar mulki ta Berlin suka fara mayarwa dangane da zaben shugaban kasar Amurka. Joschka Fischer, ministan harkokin wajen Jamus ya ce kasar zata ci gaba da ma’amallarta da kowace gwamnati da za a nada a fadar mulki ta White House. Shi kansa ministan harkokin wajen na Jamus sai da ya ji ta a jika lokacin da aka fuskanci gurbacewar huldar dangantaku tsakanin shugaba George W. Bush da shugaban gwamnati Gerhard Schröder. Musabbabin wannan sabani kuwa shi ne yakin da Amurka ta gabatar akan kasar Iraki. Mai yiwuwa a samu sauyin al’amura idan har George W. Bush ya samu ikon yin ta zarce a cewar daya daga cikin jami’an gwamnati a fadar mulki ta Berlin. Amma fa fitaccen masanin manufofin ketare na jam’iyyar SPD Hans-Ulrich Klose yayi taka tsantsan wajen bayani a game da abin da ka biyo baya a dangantakar kasashen biyu idan Bush ya zarce akan kujerar shugabancin Amurka, inda ya ke cewar:

"Abu daya da za a yi madalla da shi idan hakan ta samu shi ne kasancewar an san salon kamun ludayin shugaban na Amurka kuma a saboda haka an san yadda za a tinkare shi. To amma a inda take kasa tana dabo shi ne kasancewar shi Bush ba mutum ne da ya fi sha’awar yin gaban kansa wajen daukar matakai, a maimakon tuntubar sauran kawayen kasar ta Amurka domin gabatar da matakai na kasa da kasa."

Amma ministan cikin gida na Jamus Otto Schily na tattare da ra’ayin cewar babu wani abin da zai hana ruwa gudu a ma’amalla tsakanin Jamus da Amurka idan Bush ya ci gaba da mulkin wannan kasa. Ya ce yana da kyakkyawar alaka da wakilan gwamnatin Bush, musamman ma a fannin hadin kai domin murkushe ta’addanci a duniya. Sannan bugu da kari kuma an sha gudanar da shawarwari da musayar ra’ayoyi tsakanin shi kansa Bush da shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder. Dangantakar Jamus da Amurka na daya daga cikin shikashikan manufofin gwamnati a fadar mulki ta Berlin ba tare da la’akari da gwamnatin dake ci a fadar White House ba.

Shi kuwa Hans-Christian Ströbele dan jam’iyyar the Greens, bisa ga ra’ayinsa nasarar Bush a wannan zabe ka iya zama babbar kalubala, inda yake cewar:

Idan har hakan ta tabbata to kuwa lamarin zai zama tamkar gigin barci a gare ni. Domin kuwa a gani na hakan tamkar goyan bayan akasarin al’umar Amurka ga manufofin George W. Bush ne, musamman ma nuna amincewa da kuma goyan bayan yakin da ya gabatar kan kasar Iraki, wanda mataki ne na keta tsarin yarjeniyoyi na kasa da kasa. Duk wani mai sha’awar zaman lafiya, jikinsa zai yi la’asar idan har Bush ya ci nasarar zaben.

Daga bangaren ‚yan hamayya kuwa Volker Rühe, mai magana da yawun CDU akan manufofin ketare shi ne kadai ya furta albarkacin bakinsa, inda ya bayyana fatan kyautatuwar dangantakar kasashen kungiyar tsaron arewacin tekun atlantika NATO in har Bush ya ci nasarar zaben. Wajibi ne Bush ya nemi hadin daga kasashen Turai a maimakon kokarinsa na rarraba kawunansu.