1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ra´ayi sun banbanta kan tallafi ga Afurka

September 25, 2009

Saɓanin ra´ayi dangane da taimakon raya ƙasa ga ƙasashen Afurka

https://p.dw.com/p/JohI
Ministar taimakon raya ƙasashe masu tasowa ta Jamus Heidamarie Wieckzorek-ZeulHoto: picture-alliance/ dpa

A yayinda wasu ke da ra'ayin cewar kwalliya ta mayar da kuɗin sabulu game da wannan manufa, wasu kuma ga ra'ayinsu matakan su haifar da wani ɗa mai ido ga ƙasashen Afurka ba. A lokacin da take sharhi game da haka jaridar Süddeutsche Zeitung nuni tayi da cewar:

"Ainihin jami'an taimakon raya ƙasar ne ke da ra'ayin cewar ayyukansu na taimako a ƙasashe masu tasowa sun cimma nasara ko da yake al'amuran nahiyar Afurka na da sarƙaƙiyar gaske, inda kashi 68% ne na shirye-shiryen raya ƙasar suka cimma nasara. Amma su kansu ƙwararrun masana na Afirka, a ganinsu, su kansu jami'an taimakon ne suka ci gajiyar lamarin amma ba nahiyar Afurka ba. Saboda a ƙarƙashin waɗannan matakai sun samu guraben aikin yi, a yayinda ƙasashen dake ba da taimakon kuma suka samu wata kafa ta yin tasiri akan siyasa da albarkatun ƙasa a nahiyar."

Ita ma jaridar Die Zeit ta taɓo wannan batu inda take saka ayar tambaya a game da amfanin wannan taimako. Jaridar ta ce:

"A halin yanzu ana daɗa sukan manufofin taimakon raya ƙasa. Miliyoyin kuɗaɗen taimako da gwamnatocin ƙasashe masu ci gaban masana'antu ke zubawa a taimakon raya ƙasa, a haƙiƙa illarsu ta fi amfaninsu yawa. Galibi kuɗaɗen na kwarara ne zuwa ga 'yan gata waɗanda ke ƙara ingiza Afirka cikin talauci. A maimakon a yi amfani da waɗannan kuɗaɗe don yaƙar talauci, sai a riƙa bacaka da su, kamar dai wajen gina fadar mulki ta Bokasa ko bikin ranar haifuwar Mugabe da sauransu."

01.06.2009 global 3000 kakao

Ɗaya matsalar da ake ci gaba da saɓani kanta kuma ita ce ta aikin yara ƙanana, wanda mujallar Der Spiegel ta mayar da hankali kansa a wannan makon. Mujallar ta ce:

"A sakamakon rahotannin da ake gabatarwa game da ayyukan yara ƙanana a gonakin koko, kamfanonin sarrafa abinci ke fama da matsin lamba domin tilasta wa abokan cinikinsu su daina ɗaukar yara aiki. Amma fa hakan zai taɓarɓara rayuwar manoman koko, waɗanda a sakamakon ƙarancin kuɗaɗen shiga ba zasu iya dakatar da yaran daga aiki ba. Ba hana yara aiki ne zai taimaka a warware matsalar ba, sai dai kamanta adalci wajen cinikin amfanin da manoman ke samarwa."

Kenia Dürre bei Athi tote Kuh
Hoto: picture alliance / dpa

Ƙasar Kenya na fama da matsalar fari, wanda ke barazana ga makomar yanayin gandun dajinta na Srengeti. A lokacin da take batu game da haka, jaridar Süddeutsche Zeitung cewa tayi:

"Dubban namun daji ke salwanta, in kuwa babu su ba maganar yawon buɗe ido a ƙasar, alhali kuwa ƙasashen Kenya da Tanzaniya sun dogara ne kacokam akan yawon buɗe ido don samun kuɗaɗen shiga. Suna buƙatar waɗannan kuɗaɗe matuƙa ainun don yaƙi da talauci da gina makarantu da asibitoci da nagartattun hanyoyin mota."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Mohammad Nasiru Awal