Raɗaɗin Cutar amai da gudawa a Haiti | Labarai | DW | 17.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Raɗaɗin Cutar amai da gudawa a Haiti

Cutar Kwalara na ci gaba da ta hallaka mutane sama da dubu a Haiti na yaɗuwa a ciki da wajen wannan ƙasa.

default

Masu fama da cutar kwalara a Haiti.

Ma'aikatar kiwon lafiya ta ƙasar Haiti ta bayyana cewar adadin mutanen da cutar amai da gudawa ta hallaka ya zuwa yanzu ya zarta dubu. Kana ta nunar da cewar mutane kusan 17000 ne suka kwanta a asibiti tun bayan ɓarkewar cutar a watan oktaba.

Dubun dubatan mutane ne dai suka fantsama a kan titunan birnin Cap-Haitien domin yin Allah wadai da riƙon sakainar kashi da hukumomi ke yi wa batun na Kwalara. Mutane biyu aka tabbatar sun rigamu gidan gaskiya a lokacin da dakarun Majalisar Ɗinkin Duniya suka buɗe wuta domin kare ginin daga fishin 'yayan ƙasar ta Haiti.

Hukumomin na Haiti na ci gaba da ƙoƙarin daƙile cutar ta amai da gudawa da ke kassara al'uma watannin goma bayan bala'in girgizar ƙasa da ta hallaka mutane dubu 250. A halin da ake ci cutar ta kwalara ta yaɗu zuwa Jamhuriyar Dominikan inda aka bayar da sanarwar cewa mutum guda ya kamu da ita a tsibirin Hispaniola da ke kan iyakar ƙasashen biyu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Umaru Aliyu