Queen Njinga Mbande - Jami′ar diflomasiya gwarzuwa a fagen yaki | Tushen Afirka: mutanen da suka taka rawa a tarihin Afirka | DW | 13.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Tushen Afirka

Queen Njinga Mbande - Jami'ar diflomasiya gwarzuwa a fagen yaki

Jami'ar diflomasiya kuma shugabar sojoji a karni na 17, Njinga Mbande ta yi duk me yiwuwa wajen yakar Turawan mulkin mallaka daga kasar Potugal.

Rayuwa: Ta rayu a kasar da a yau ake kira Angola bisa kiyasi an haifata a shekarar 1583 a yankin Ndongo, ta mutu a ranar 17 ga watan Disambar 1663 a yankin Matamba.

Fagen da ta yi fice: Ta karar da rayuwarta wajen yaki da Turawan mulkin mallaka daga Potugal ta hanyar amfani da kwarewarta a fannin diflomasiya da ma aikin soja a karni na 17 a yankin da ke a karkashin Angola a wannan lokaci.

Sukar da ake mata: Halayyar rashin imaninta da ya hada da kisan dan dan uwanta a kokarinta na samun mulkin Ndongo da harkokin cinikin bayi da cimma huldar kasuwanci ta tura bayi ga Turawan Potugal da na Holand uwa uba ga zarginta da halayyar cin naman mutane wato koyi da halayyar kawayenta mayakan Imbangala.

Njinga ba ta mika wuya:

A shekarar 1622 me sarauta Ngola Mbande wato dan uwan Njinga ya aikata zuwa Luanda don kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin yankin Ndongo da gwamnan Potugal, an mika mata darduma don ta zauna maimakon kujera abin da ke nuna cewa an kaskantar da ita, nan Njinga ta nemi daya daga cikin bayinta ya durkusa kan gwiwarsa ta zauna a bayansa tamkar kujera, aka ci gaba da kulla yarjejeniya da ita ba tare da jin ta koma baya ba.

Njinga me ilimi: Ta lakanci harsuna da dama na al'ummarsu haka nan ta iya harshen Turawan Potugal, tana da ilimi don haka hatta rubutu na tattaunawar da ake da ita da Turawan da kanta take rubutawa. Samun alaka da 'yan mishan tun da fari da ma Turawan Potugal 'yan kasuwa, sun taimaka mata a wannan fanni. Tana da gogewa ta diflomasiya ga sanin harkokin soja duk sun taimaka mata a alaka da Turawan Potugal da Holand.

Njinga gwarzuwa: Njinga an gabatar da ita a fagen yaki a madadin babanta Sarki Kiluanji, a lokacin mulkinta ta kan yi yaki a matsayin soja abin da ke nunata a matsayin mace da kamar maza.

A cewar wasu masana tarihi Njinga daga baya ta ki karbar sarauta a matsayin sarauniya face a kirata da sarki, a zamantakewa ita namiji ce, inda ta tara maza a matsayin kuyangi suna sanya kaya tamkar mata.

Wadanda suka yi hidima wajen hada labarin: Carla Fernandes da Gwendolin Hilse. Wannan bangare ne na shiri na musamman Tushen Afirka "African Roots", Shirin hadin gwiwa tsakanin tashar DW da Gidauniyar Gerda Henkel.