Pyongyang ta nuna rashin jin daɗinta | Labarai | DW | 22.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Pyongyang ta nuna rashin jin daɗinta

Koriya Ta Arewa ta ce atisayen sojin tsakanin Amirka da Koriya Ta Kudu barazana ce ga zaman lafiyar duniya

default

Hillary Rodham Clinton da Robert Gates, lokacin ziyararsu a Koriya Ta Kudu

Gwamnatin Koriya Ta Arewa ta yi kakkausan suka ga shirin gudanar da atisayen soji na haɗin guiwa tsakanin Amirka da Koriya Ta Kudu a gaɓar tekunta da cewa barazana ce ga zaman lafiyar duniya. Wakilin Koriyar Ta Arewa a taron gamaiyar ƙasashen kudu maso gabashin Asiya dake gudana a birnin Hanoi na ƙasar Vietnam ya ce irin wannan atisayen na zama karan tsaye ga tsaron yankin tsibirin Koriya. Jami'in yayi kira ga Amirka da mayar da hankali akan sharuɗɗan sake komawa kan teburin shawarwari game da shirin nukiliyar Koriya Ta Arewa. A ranar Asabar mai zuwa ake shirin fara atisayen tsakanin Amirka da Koriya Ta Kudu a tekun Japan. Tun da farko sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton da sakataren tsaro Robert Gate sun yi kira da a sanya gwamnatin Pyongyang ƙarin takunkumi domin hana ta faɗaɗa shirinta na nukiliya.

"Koriya Ta Arewa za ta iya daina halayar tsokana da nuna barazana ga maƙwabtanta. Za ta iya ɗaukar matakan yin watsi da shirinta na nukiliya kana ta yi biyayya ga dokokin ƙasa da ƙasa. Idan ta bi wannan hanya za a ɗage mata takunkumai."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Zainab Mohammed Abubakar