Pyongyang da shirin rage makaman nukiliya | Labarai | DW | 10.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Pyongyang da shirin rage makaman nukiliya

Koriya Ta Arewa ta bayar da kai ga bukatar MƊD ta tattaunawa domin kaw da makaman ƙare dangi a duniya

default

Koriya Ta Arewa ta amsa kirar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi mata ta komawa kan teburin tattaunawa, domin kawo ƙarshen takun saƙa da ke wakana game da makaman nukiliya da ta mallaka. Kakakin ma'aikatar harkokin wajen ƙasar, ya ce fadar mulki ta Seoul a shirye ta ke, ta ci gaba da neman bakin zaren warware taƙaddamar tare da haɗin guiwar wasu ƙasashe shida na duniya. Majalisar ta Ɗinkin Duniya ta nemi Koriya Ta Arewar da shiga cikin sahun ƙasashen da suka mallaki makamin ƙare dangi da za su yi ƙeƙe da ƙeƙe, da nufin cimma yarjejeniyar kawar da makaman nukiliya a duniya. Tun a shekara ta 2007 ake fuskantar cijewar lamurra dangane da cimma matsaya tsakanin ƙasashen da suka haɗa da Amirka da Japan da Rasha da China da kuma Koriya Ta Arewa da kuma takwararta ta Kudu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe

Edita: Mohammad Nasiru Awal