1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Putin zai kauracewa taron sulhunta rikicin Siriya

Ramatu Garba Baba
January 26, 2018

Rasha mai masaukin baki a taron tattauna mafita kan rikicin kasar Siriya, ta ce shugaba Vladimir Putin ba zai hallaci taron da zai gudana a Sochi daya daga cikin manyan biranen kasar ba.

https://p.dw.com/p/2rZFL
Russland Präsident Putin empfängt Syrien-Veteranen im Kreml
Hoto: Reuters/K. Kudryavtsev

Kakakin gwamnatin Rashan Dmitry Peskov ne ya sanar a wannan Juma'ar,  ya ce taron na da matukar mahinmanci amman kuma shugaban kasar ba zai shiga zaman ba, bai kuma fadi dalilin da ya sa Putin zai kauracewa taron da ke kokarin warware rikicin yaki na basasa da Rashan ke taka rawa ganin ta na da rundunar soja da ta jibge a Siriya don yakar masu tayar da kayar baya.

A mako mai zuwa ne aka shirya zaman taron don bai wa bangarorin da ke rikici da juna da kuma masu mara musu baya musanman Rasha da Amirka lokaci don daidaita matsayarsu kan kawo karshen rikicin na fiye da shekaru shida. Yakin basasan ya lakume rayukan daruruwan mutane da kuma tilasta wasu miliyoyi zama 'yan gudun hijra.