1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Putin ya sha alwashin farfado da tattalin arzikin Rasha

Zainab Mohammed Abubakar GAT
May 7, 2018

Vladimir Putin ya sha rantsuwar zarcewa a kan kujerar shugabancin Rasha na wasu karin shekaru shida. Wannan shi ne wa'adinsa na hudu kan kujerar shugabancin kasar ta Rasha.

https://p.dw.com/p/2xJLY
Russland Putin Amtseinführung
Hoto: Reuters/Sputnik/A. Nikolskyi

Dubban Rashawan sun hallara a fadar shugaban kasa ta Kremlin suna ta rera taken kasar bayan da Shugaban Vladimir Putin ya sha rantsuwa ta cigaba da mulkin kasar har tsawon shekaru shida nan gaba.

 " A matsyina na shugaban Tarayyar Rasha, a yau ina rantsuwa wajen tabbatar da kare 'yanci da al'umma, zan tabbatar da tsaro da kare martabarku bisa tanadin kundin tsarin mulkin wannan kasa tamu".

Bayan tsawon shekaru 18 kan kujerar mulki, Putin ya lashe zaben da ya ba shi damar ci gaba da kasancewa shugaban Rasha na karin wasu shekaru shida, bayan ya lashe zaben da ya gudana a watan Maris, inda ya yi nasarar samun kashi 77 daga cikin dari na kuri'un da aka kada. 

Ya ce farfado da tattalin arzikin kasar da ya sukurkuce sakamakon takunkumin kasa da kasa da aka gindaya wa Rashan, shi ne batu da zai sanya fifiko a kai:

" Ina ganin hakki ne da ya rataya a wuyana in sadaukar da rayuwata wajen yi wa Rasha aiki, a yanzu da ma shekaru masu gabatowa. Muna muradin zaman lafiya da cigaban kasa, ta yadda za mu ci gaba da tabbatar da martabar kasarmu, domin zamantakewa a matsayin iyali guda".

Inauguration Putin Gerhard Schröder
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Druzhinin

Duk da cewar Vladimir Putin ya maido da martabar Rasha a idon duniya a fannin ayyukan soji, ya sha fuskantar suka dangane da dogaron kasar kan kudaden da take samu daga fitar da mai da makamashin gas, wajen gina sashen masana'antu. Sai dai a cewar shugaban kasar kamata ya yi Rasha ta tafi daidai da zamani, ta yadda za ta karbi duk abun da ya zo mata:

" Wajibi ne mu yi amfani da dukkan damarmaki da ke da akwai, na farko shi ne, magance batutuwan da suka shafi cikin gida da cigaba, saboda tattali da bunkasa harkar fasaha, wadanda su ne za su ba mu damar gogayya a fannonin da su ne tankar makullan shekaru masu zuwa."

Jawabin nasa dai bai tabo matsayin Rasha a ketare sosai ba, fa ce furta cewar Rashan na da karfi, himma da kuma mai arongizo a'lamuran da suka shafi kasa da kasa. Putin ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tabbatar da matsayin kasar a fannin tsaro da kariya, ta hanyar ci gaba da mayar da hankali kan wannan bangare.

Shugaban na Rasha a daya hannun ya nemi 'yan majalisar kasar da su ba da goyon bayansu wajen amincewa da Dmitry Medvedev a matsayin framinista .

Russland Präsident Putin
Hoto: picture-alliance/TASS/M. Klimentyev

Tun daga farkon karni na 21 ne dai Putin ya hau karagar mulki, sai dai ya sauka a shekara ta 2008, saboda cikar wa'adin mulkinsa. Sai sai an nada shi framinista, inda ya ci gaba da jan akalar mulkin kasar har zuwa lokacin da ya sake karbar madafan iko a matsayin shugaban kasa a shekara ta 2012.