Putin na tsammanin ziyarar Merkel a Rasha | Labarai | DW | 16.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Putin na tsammanin ziyarar Merkel a Rasha

Wannan ganawa dai na zuwa ne bayan da dangantaka tsakanin kasar ta Rasha da Jamus ta yi tsami saboda yadda Jamus ta goyi bayan sanya wa Rasha takunkumi.

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya bayyana cewa ya na tsammanin Shugabar gwamnatin Jamus za ta kai masa ziyara a watan Mayu. Shugaban ya bayyana haka ne a wannan rana ta Alhamis a lokacin da ya ke ganawa da gwamnan jihar Bavaria Horst Seehofer.

Wannan ganawa dai na zuwa ne bayan da dangantaka tsakanin kasar ta Rasha da Jamus ta yi tsami saboda yadda Jamus ta goyi bayan sanya wa Rasha takunkumi inda a bangare guda ta ke mara baya ga kasar Ukraine wacce Jamus ke kallo a matsayin wacce mahukuntan Rasha ke wa kutse.

A lokacin da ya kai ziyara a makon jiya ministan harkokin wajen Jamus Sigmar Gabriel a birnin Moscow, Shugaba Putin ya ce ya na son a inganta dangantaka tsakanin kasashen biyu. Wannan na zuwa ne adaidai lokacin da Shugabar gwamnati Merkel ke shirin zuwa Amirka.