Puigdemont ya mika kansa ga hukumomi
November 5, 2017Talla
A yanzu dai babban mai gabatar da kara na kasar Beljium ya ce za su ci gaba da yin nazari kan takardar somame da Sapaniya ta aikewa kasar. Nan da lokaci kadan alkalin zai yanke hukunci kan jagoran 'yan awaren na Kataloniya da sauran mutanen hudu, domin sanin ko za a ci gaba da tsare su ko za a ba da belin su a kan wasu ka'idoji. Spain:Sammaci ga shugaban yankin Cataloniya
A tun ranar Jumma'a ne dai Carles Puigdemont ya tsere daga kasar Spaniya zuwa neman mafaka a kasar Belgium, bayan da mahukuntan Spaniya suka haramta zaben neman kafa yankin Kataloniya.An fara shari'ar maharan Spain